Babi na 12_ Safiya Huguma

3.4K 264 24
                                    

KUNDIN HASKE

AL'KALUMAN MARUBUTAN HASKE

HASKE WRITERS ASSOCIATION

BABI NA GOMA SHA BIYU

*MUTUNCIN MACE........*

*TARE DA ALQALAMIN....*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


    Tsaye take a madaidaicin garejin gidan nata  tana fuskantar motar qirar matrix wanda maigidanta ke zaune a ciki yana yunqurin kunna motar,baki daya a qage take,Allah Allah take ya kammala kunna motar ya rufe ta ya fice daga gidan,tsayawar da yayi yana jiran motar ta dauki zafi ma gani take kamar da gayya yayi hakan,kamar ta tunkudashi ya fice haka take ji,saidai dole ta saki jikinta ta lallabashi har ya fice,don bata manta gargadin da ya sake yi mata kwana uku da suka gabata ba.

    Sai daya kammala komai sannan yaja murfin motar ya rufe,a dawo lafiya ta masa ya amsa sannan yace
"Ina fatan baki mance da abinda na gaya miki ba". Kai ta gyada cikin zaquwa
"eh in sha Allahu"
"Kifin nan na jiya,inaso kimin farfesunsa shi zan fara ci idan na dawo bayan an sha ruwa" kasancewar yana azumin litinin da alhamis
"Babu damuwa" ta fada tana boye k'aguwar da tayi ya fice
Daga haka bai sake cewa komai ba yaja motar da baya ya fice daga gidan.

     Da hanzarinta ta koma cikin gida a sukwane idanunta kan agogo,qarfe tara ta gani da minti biyar,ta dan bude baki alamun mamaki,cikin hanzari ta shige uwar dakinta tana magana ita kadai cikin ranta
"Nasan yanzu kowa ya fito ni kadai ce na makara" ta qarashe zancan tana yunqurin daukar 'yarta dake kwance tana bacci kan gado,sai data goyata a bayanta sannan ta dauki zaninta dakw gefe ta daura saman doguwar rigar baccin dake jikinta,ta dauki hijabi ta zura tana laluben maqullin gidan
"Mama....kashi nake ji"waiwayowa tayi,sai sannan ta tuna da daya yarin yar tata data baro a kitchen lokacin da take mai gidan rakiya,fuskarta ta bata don ta lura yarinyar na shirin sake bata mata lokaci ne kawai duk saurin da take yi
"kinga,maida wandonki idan munje gidan anty rakiya kyayi" diddira qafafunta yarinyar ta soma tana gaya mata ya matseta amma sai ta daka mata tsawa,tilas yarinyar ta maida wandon nata tana kwabe fuska,ta dauki muqullan gidan taja hannun yarinyar suka fice ba tare data damu da kauda ko tsinke daga gidan nata da niyyar gyara ba.

   Gida na hudu dake bayan layin nasu ta shiga,tun daga soron gidan zaka fuskanci gidan cike yake da mata,duk da a lokacin duka duka baxai wuce qarfe tara da kwata na safe ba,sallamarta ya sanya sauran matan da aqalla sun kusa goma sakin shewa tare da yi mata maraba da zuwa,wasu na fadin ga badariyyan nan,fuskarta dauke da fara'a kamar wadda aka yiwa wani albishir da shige cikinsu suka soma gaisuwa,zaman dirshan tayi gefan tabarmar data taddasu kai tana kwance goyonta,baki daya matan kamar yadda take su dinma haka suke,dai daikun cikinsu ne kadai shigarsu zata nuna maka sunyi wanka,ko daidaita a zaman nata bata yi ba wata mace wadda tadan fisu a shekaru tace
"Hajiyata ke muketa jira fa,muna nan muna musu da maman kubra,yi musu bayani don Allah ya kijaji maganin"
"Ah ai jiya ansha shagali in gaya miki hajiya......maganin nan kam babu gaibu a ciki" shewa suka saki baki daya kowacce na bada kunne da hankalinta ga badariyya tare da tofa albarkacin bakinta
"Ku saurara,magani fa duk maiso kawai ta karba,kunsan yau sai da baban khairat ya tafemin dubu biyar cash da safiyar nan?" Take suka sake hautsine,muryar hajajju wadda ita ta kawo maganin muryarta tafi ta kowa fita cikin farinciki tace
"Ahto,ai na gaya miki,matuqar zaki dimanci amfani da magunguna na ba fada ba ko kallon banza yabar miki,kuma ko zaki kwana kiba zagaye unguwar nan da sunan yawo yabar ganin laifinki bare ya miki fada,balle ma mu zaman qaruwa da juna muke"
"Ai bari kuji..." Badariyya tayi wani zillo tana gyara zama,nan ta soma fayyace musu duk wani abu daya faru tsakaninta da abban khairat a daren jiya ba tare da tayi duba da yaran da suke wajen wadanda iyayensu suka taho dasu ba,dududu yaran daga shekara takwas ne zuwa qasa.

     Hira tayi hira,sam baki daya ta mance da husna 'yarta wadda suka shigo da ita tanajin bayan gida,sai wajejen shabiyu da mintina na rana sannan yarinyar ta sake kwasowa a guje ta iso gefan uwar ta tsaya tana cewa
"Mama....nayi kashin" waiwayowa tayi tana duban yarinyar kamae zata maketa saboda ta katse mata hirarsu da take ci gaba da daukan dadi,ba tare da daya daga cikinsu tayi niyyar waiwayar gida ba,duk kuwa da cewa a kwai masu qananun yara a cikinsu
"Don ubanki shine kika yimin kashi a wando?,wallahi sai naci ubanki kuwa tunda na hanaki bakya jin......", kafin ta qarasa maganar tata wani matashin almajiri da aqalla zaiyi shekara sha hudu zuwa sha biyar yayi sallama riqe da hannu wata yarinya da ba zata wuce shekara takwas ba sanye da unifoarm goye da jakar makaranta,hannunsa riqe da lunch boxs din yarinyar,cike da farincikin ganinsa tace
"Yauwa auwalu sun taso,ungo don Allah" ta fada tana miqa masa muqullin gidan
"Ka tafi da husna ma baki daya don Allah tayi kashi ka wanke mata,kayi mata wanka don ban samu dama ba,ka gyara kitchen ka wanken tsakar gida kayi wanke wanke,idan ka gama sai kazo ka yikin cefanen,kada ka bar khairat da unifoam ka shiga dakinsu don Allah ka dauko mata wasu kayan ta canza,gani nan zuwa"
"To anty" ya fada yana karbar muqullin
"Nikam yau sha'awar romon kifi nake wallahi,koshi zamu dafa ne?" Lariya matar gidan ta fada tana kallon sauran matan dake zazzaune
"Eh wallahi,saidai yanzu da qyar idan za'a samu danye,saboda rana ta soma yi qila sun fara soyawa....saidai ko wajen maman khairat ba za'a rasa ba,jiya kaman ledar kifi na gani gun maigidanki da magariba yana dawowa" cewar maimuna daya daga cikinsu,
"Ai baban khairat badai cin dadi ba,kullum ba'a rasa gidanshi da kifi ko nama"murmushin jin dadi badariyya ta saki,saboda ko banza an fasa mata kai an kankarota cikin mutane
"Kifi ne kuwa,yana nan a cikin fridge na cilla shege ko gyarashi banyi ba,bari nasaka auwalu ya taho mana da shi"
"Yauwa hajjaju,amma fa ban da kalanzir"
"Ba matsala sai ya hado mana da qaramin gas dina mu dafa a nan"
"Na bayar da mai da maggi" cewar habiba wadda ke zaune gefe tana sauraronsu,a duniya tana kishin yadda ake fasawa maman khairat kai a cikinsu,shi yasa itama take yunqurin wani abu don a yabeta itama duk da mijinta baida qarfin mijin maman khairat din.

    Shewar dadi suka sa kowacce na nuna farincikinta,ko banza yau zasu murqushi dadi,qwalawa auwalu kira tayi kafin ya kai ga fita ta gaya masa abinda zai dauko din,ya amsa da to yaja hannun yaran ya fice da su.

*mrs muhammad ce*👑

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now