Shafi na biyu

2.3K 194 9
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL-K'ALUMAN MARUBUTA...*

✍🏻

*_NA KUNGIYAR:-_*
     _HASKE WRITERS ASSO...._

*TAREDA AL-K'ALAMIN...*
       *_Nana Hafsat_* _(MISS XOXO)_

*_🙆🏻‍♀NI NA JAWA KAINA!!😭_*
(SHAYE SHAYEN MAGANIN MATA)

*BABI NA BIYAR.*

     *SHAFI NA BIYU...*

“Abban Zara'u yau ne sunan yaron anty Saddiqa,idan su Zara'u sun taso makaranta zamuje”

Kallonta yayi, yayinda rabin hankalinsa kekan dai-daita hular zanna Bukar akansa.

“Nafisa kedai nakula bakya gajiya da yawo kokad'an,naga kwana uku daya wuce kikaje wani sunan? shin bakya ganin kina tauyewa Zara'u hakk’i kuwa? kamata yayi idan tadawo taje islamiyya, amma kina maganar tafiya da ita gidan suna?”.

“Abban zara'u kasan dolene naje sunannan, inba hakaba dangi zasuyita k'orafi banason shiga danginka. maganar zara'u kam nima banason tana fashin islamiyyar, amma kaga aii babu yanda za'ayi nabarta ita kad'ai, tunda k'arfe 5 suke tashi........”

Juyowa yay yana kallonta da sauri, tareda k'atseta..
   
“oh kekuma sai k'arfe nawa zaki baro gidan sunan kenan? dahar kike ganin Zara'u za'a tasosu bakya nan?"”

Shiru tayi,dan batada amsar dazata bashi.

Yagama fesa turare sannan yamatso kusada ita,

“shikenan saikun dawo,ga wannan saikiyi kud'in napep,wannan kuma kibata, amma kudawo dawuri”.

Tsalle tadaka,tareda rungumesa tana godiya,

Murmushi kawai yayi,yajanyeta ajikinsa,

“bara kiga nawuce kasuwa rana tanayi”.

“To”
Kawai tace ta matsa daga jikinsa.

Yafita zuciyarsa na mamakin halin Nafisa,kokad'an batasan fad'ama miji adawo lfy ba,ko gaisuwar safe bata iyaba itakam,shiyyasa ga Zara'u nan tatashi da wannan tarbiyyar,yarinyar batasan ta gaidashiba.Aganinsa ba kula dashi agado kawai yakamata tayiba,taringa had'awa dawasu abubuwan,dan maganar gaskiya Nafisa tanada raunin kulawa dashi azamantakewarsu,amma tana kula dashi a shinfid'a.

******

Ana taso su Zara'u daga makaranta tashiryata, itama tashirya cikin kwalliya suka tafi gidan sunan yaron Aunty Saddiqa yayar Baban Zara'u.

*GIDAN SUNA*

  Gidan sunan kam harya fara tara jama'a, musamman ma 'yan uwa na kusa da k'awayen mai jego.Gaisuwa tashigayi dasu,yayinda sukuma suketa jan Zara'u jikinsu. ta gaisa da mai jego sannan tabata abinda Baban Zara'u yabata,daga nankuma tazauna anata hira.

Can labari yay dad'i har akazo kan hirar maganin mata.

Kunsandai mata in antaru...

Wata tace,

“kai jama'a ad'an bamu sirrin mana, kunata hirar kayan shagali amma kun barmu baya?”
  
Dariya aka shek'e da ita, sunata tafawa.

Maman Zara'u tace,

“Ai  kayan harka sai hajjaju,wanifa had'i databani ranar,hummm ba'a magana.”

Masu karatu na k’ark’are maku xance de haka maman Zara'u tasaki baki taita zuba zance,mata na shewa da dariya, tareda jinjinamata.

Suma sauran suka shiga bada labarin nasu,ana tsak'a dawannan hira saiga wata mai kayan mata takawo.

Nanfa mata akaita rawar jikin saya wad'anda suka ta6ashan irinsa sai labarin maganin suke badawa da aikinsa....

Kankace me mata tasaida komai tas, tacika aljihunta da kud'i tayi gaba abinta, su Maman Zara'u kuma aka nad'o magunguna akadawo gida.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now