Shafi na bakwai

2.2K 267 25
                                    

*MUTUNCIN MACE........*

*TARE DA ALQALAMIN....*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

        0⃣7⃣

    Su uku ne suka fito fuskarsu da sautinsu k'unshe da dariya,husna ce a gaba sanye da riga da wando masu kyau,ire iren kayan da tunda yake siyama yaranshi don ayi musu ado,sai matar biye da husna tana gyara mata ribbom d'in kanta daya zame tanawa usman dake biye da ita cikin jallabiyya mai kyau mai dogon hannu magana cikin dariya dariya yana amsa mara,da alama zolayar juna suke.

     Muk'ut ta hade wani yawu da k'yar saboda yadda kishi ya cushe mata mak'ogaro da kafar numfashi,usman din nata gani take tamkar bashi ba,ya sauya yayi wani irin kyau,k'uruciyarshi ta sake fitowa.

       Yana d'ora idanunshi a kanta fara'ar fuskarshi ta b'ace b'at,abu d'aya ya tuna wanda ya hanashi juyawarshi ya koma,sai ya k'araso falon can nesa ya zauna cikin d'aure fuska,wanda hakan ya sanya amaryar tashi nusaiba cikin duhu,tafiyar husna cikin dariya wajen badariyyan tana kiran
"Laaaa...mama" shi yakai matar gano,kishi ya d'an soketa kad'an amma tayi yunk'urin dannewa,duk da haka itama sai fara'ar fuskarta ta ragu,ta juya zuwa cikin kitchen d'in dake manne da falon don samawa badariyyan ruwa tunda ance bak'onka annabinka.

      Idanunta da suka cika da qwalla take kallon husna da su tana shafa kwantaccen gashinta daya samu wadataccen gyara,da yake yaran nata akwai albarkar suma,kada ma marigayiya khairat taji labari don har tafi husna,yanayin yarinyar tata ya burgeta,fes da ita k'amshi na fita a jikinta kaman ba husnarta ba,ba zata iya tuna sau nawa yaran nata suka kasance cikin wannan kamar ba sanda take tare da su,cike da kunya da mamaki ta amsa gaisuwar da husnar ke mata bayan ta durk'usa gabanta,iya saninta bata tab'a ma samun wani lokaci da zata tsaya ta koyar dasu gaida babba ba,koda babansu ne kuwa,shine ma wani lokaci yake koya musu duk sanda buk'atar hakan ta kama.

      Da lemo da ruwa nusaiban ta dawo ta aje mata kana ta dubi usman
"Barin shiga na gyara ciki ko?" Ta fada ne kawai don ta basu waje batasan me ya kawo ta ba,nuni ya mata da gefansa,ko bai fadi ba tasan me yake nufi,bata saba masa musu ba saboda haka ta koma gefanshi kan kujera two sitter ta zauna,duk da ta bada gaf a tsakaninsu amma hakan sai ya sanya badariyya jin ta muzanta,gaidashi tayi ya amsa kadaran kadaham yana karbar khairiyya dake hannun husna yana duba yarinyar,bai sake ganinta ba tun wancan lokacin sai yau,duk da yana aikawa da duk wani abu da yarinyarshi zata buk'ata amma b'acin rai da rashin son ganin badariyya vai barinsa ya tsaya neman ganinta
"Dama husna nazo gani" sai ya mik'e yana fad'in gata nan ai"yana mai wucewa zuwa ciki,duk ita da nusaibar suka bishi da kallo,sai nusaiban taji ba dad'i,binshi tayi ta masa magana kan abinda yayi,nuna mata yai baison zancan saboda haka ta k'yaleshi ta dawo falon.

      K'ok'arin sakin jiki tayi da badariyyan suka d'an taba hira da bata wuce ta minti goma ba,wadda duka hirar kan husna ne,ta miqe zata tafi nusaiba ta karbo mata khairiyya da kudaden daya had'o yarinyar da shi,bayan ya bata sak'on ta gaya mata ba sai ta sake zuwa ba indai husna ce duk sanda suje free za'a dinga kawota,saboda duk sanda yaga badariyyan sai ya tuna b'acin ran da suka shiga watannin baya ta silarta,nusaiba kam kasa gaya mata hakan tayi,har bakin get ta rakata,ta waiwayo tayi mata godiya kan yadda taga ta riqe mata husna
"Haba,ba komai,ai d'a na kowa ne,bare kuma d'an ma na usman ai ya cancanci ka rik'eshi ko ba kai ka haifeshi ba" jinjina kai tayi tana nanata maganarta cikin zuciyarta,haka yake,usman ya cancanta don ya cika d'an halas d'in miji da kowacce mace zatayi kwadayin samu,banda shashashar mace irinta da tayi wasa da tata damar.

      Tana tafe tana goge k'walla wanda har cikin zuciyarta sai tayi dana sanin zuwa,kishi sosai ya dinga damunta,saidai bata ji haushin kowa ba don ta sani cewa ba wani ya jaza mata ba ita ta jazawa kanta duk abinda ya sameta.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now