BABI NA 13_Ummu Basheer

2.5K 161 5
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Haske Writer's Association*💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

   *RAYUWAR WASU MA'AURATA...*

  *NA*

*UMMU BASHEER*

  *Babi na goma sha uku*



Page 1

....Tun daga bakin gate yake Jin tashin kid'a.  Ranshi ya b'aci sosai.  A hankali yayi parking tare da fitowa cikin motar ya nufa cikin gidan. 

Tun daga bakin kofa ya fara cin karo da ledojin chocolates.  Biscuits da robar ice cream.  Ga kuma bottles na coke da fanta.

Parlour'n yayi kaca kaca ba kyan gani.  Da kyar ya karasa ya dauki remote control ya kashe wakar. 

Zama yayi a kujera tare da kwala Kira "Ramla,  Ramla "

An dauki 2 minutes kafin wata kyakyawar mace ta fito daga cikin wani bedroom.  Sanye take da doguwar riga kai babu dankwali.  Tana rike da waya tana dannawa.  Tana taunar chewing gum.  Ji kuke Kass Kass Kass.

Zama tayi a two seater tare da daura kafa daya kan daya.  Ta cigaba da danna wayar ta.

Kallon ta yayi Ranshi a matukar b'ace. 

"Dutse ne ni ko Kuma icce?"

Waigowa tayi "oh Sorry darling.  Yaushe ka dawo?"

Mikewa tsaye yayi  cikin bacin rai ya fara magana " Sau nawa zanyi miki warnings akan bana son in dawo Inga gidan nan haka.  Sannan kin cika min gida da kid'a kamar studio.  Ramla sai yaushe Zaki canza halin ki ne? "

Ganin tana danna waya bata kula shi ba.  Yasa ya wuce bedroom straight. 

Yana zuwa yayi wanka ya shirya ya fito.

Dinning room ya nufa.  Sai dai abin takaici.  Babu komai akai.

Still tana zaune a kujera ya same ta.

"Where's my Dinner? "

Tana yatsina fuska tace "Yau laminde bata zo ba.  So babu abinci"

"To  Ke Meye ya Hana kiyi? "

Gyara Zama tayi "Kasan fa baka aure ni Dan na dinga maka bauta ba. Kasan cewa Sarai ko a gidan mu bana girki.  Ni ba wahalaliya bace"

Cikin fushi yace " Yanzu kiyi min girki shine wahalar?  Da kike cewa ba bauta kika zo yi ba ai kinsan cewa aure ibada ce "

Mikewa tayi tsaye tana daga mai hannu " Milhan dakata.  Wallahi ni ba zan dinga maka wahala ba. Kullum da irin fad'an da kake yi yau kace wannan gobe kace wannan to bazan Iya ba" tana fadin haka ta shiga bedroom.

Zama yayi tare da dafe kai cikin takaici.

Daukar key yayi ya nufa Restaurant acan yayo take away.  Ya dawo gida yaci. 

Bai kara bi Takan Ramla ba ,ita ma bata neme shi ba.



********************











Wata kyakyawar mace ce fara . Doguwa tana sanye da material pink and blue na Riga da skirt.  Tayi parking gashin ta. Tana gyara dining table da alama an gama breakfast ne.

Can ta shiga wani bedroom. 

A gaban madubi naga wani kyakyawan saurayi Yana sa riga.  Karasawa tayi tare da taya shi sa bottoms din.  Murmushi yayi yace " Mata ta abar alfahari na "

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now