3

119 19 1
                                    

*KUNDIN HASKE*💡

*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

    *ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

    *NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)

                        *3*

Cikin tashin hankali Alhaji Bashir ya kwantar da ita ya ma rasa me zai yi saboda ruɗewa, can ya nufi firji a gigice ya ɗauko ruwa mai sanyi ya zuba mata a fuska ajiyar zuciya ta sauke ta miƙe za ta fita da sauri ya rungumeta ya shiga tofa mata Addu'o'i da haka barci ya yi awan gaba da ita, zuba mata idanu ya yi ya na tunanin zuci. To wai wa ya ke neman ganin bayan su? Sun sa ce Maryam duk da haka ba su daddara ba sai sun salwantar mishi da mata? Ina Allah ya fi su. Ya miƙe ya ɗauki wayarshi ya shiga neman layin malamin shi, "Assalamu alaikum" wa alaika salam  Alhaji Bashir yanzun nan na ke shirin kiranka sai gashi ka kira, da fatan dai lafiya? Nan ya shiga sanar da malamin tashin hankalin da ya kara Ƙunno musu. Shiru malam ya yi zuwa can ya ce "Bashir wannan lamarin ya na buƙatar addu'a saboda na ƙara yin Istihara aljani ne ya auri Maryam ban san tun yaushe ya ke jikin ta ba amma tabbas ya jima sosai har ya mayar da ita matarshi, shi ne ma ya ta fi da ita zai dawo da ita da izinin Allah da kuma ƙarfin ayyar Allah, yan zu haka na kira wani Abokina da ya ke maradi na ce ya sanar da sauran malamanmu su tayamu da addu'a, abinda kawai na ke so da kai ka yawaita sadaka da kuma nafilfili kai da matarka ku ɗinga saka karatun Alqur'ani barci bai sameku ba Bashir nima zan duqufa ganin mun ceto rayuwar yarinyar nan In shaa Allah." To malam mun gode sosai Allah ya kara girma da haka suka gama wayar ya miqe ya bar gidan.
_________

Takardu ne birjik a gabanshi amma ya kasa aiwatar da komai saboda tunanin halin da matarshi ta ke ciki, Almustapha kenan ya rame ya yi baƙi ya wani ajiye gashin baki babu can gani duk kamaninshi sun canza, iskar bakinshi ya fesar ya na jin bakinciki a zuciyarsa, wai dama haka auren ya ke? Hawayene ya shiga zubo mishi bai damu da ya goge su ba kanshi ya qwantar bisa teburin gabanshi ya cigaba da kuka tamkar karamin yaro,

"Haba Almustapha so nawa zance maka kuka ba shi ne maganin matsalar da kake ciki? addu'a zamu ɗage da yi shi ne kawai mafita a garemu." Inji Ismail shigowar sa kenan ya iskeshi cikin wannan halin,

"Ismail ba za ka ga ne ba ne wallahi ina cikin tashin hankali duɓeni fa kaga yadda na dawo, duk a rashin Maryam amma kana maganar na kwantar da hankali na? Ai ba zan taba dawo daidai ba matsawar ba a san halin da Maryam ta ke ciki."

Na sani Almustapha amma ka sani duk sanani ya na tare da sauki, Allahn da ya dora maqa shi zai ya ye maka nasiha sosai Ismail ya shiga yi mishi duk jikin shi ya yi sanyi wani irin natsuwa ya shige shi da haka suka bar ofis ɗin kowa ya shiga motarsa domin ya ta fi gida.
___________

Maryam
Daƙin da aka ajiyeta ko tafin hannunka baka gani saboda duhun yayi yawa ta na dai jin maganganun mutane da kuma almar tafiyarsu amma bata ganinsu, wani yare su ke yi wanda ba ta ganewa tun ta na jin tsoro har ta daƙe, idan za a bata abinci kawai ake ɗan daga window a miƙa mata abar mata ɗan hasken window saboda taga hasken, ba ta iya cin abincin saboda baida can gani wani ruwa ruwa ne sai shegen kazani ada ba ta ci amma da ta ga uwar bari haka ta ke ci ta na kuka wani lokacin harda toshe hanci, duk ta fita haiyacinta ta yi wani irin rama tamkar wace ta yi jinya gashin kanta ya yi duƙun duƙun saboda rashin gyara duk kamaninta sun canza sai idanuwanta da su ka kara girma sai ka Kura mata idanu za ka iya ganeta.

Abinda ya ke ba ta mamaki da kuma al'ajabi duk dare sai ta ji alamar ana saduwa da ita amma fa ba ta ganin kowa saboda duhu, ya Allah ka qubutar dani ta ji ta furta nan ta shiga yin wasu addu'o'i sai ta ji sanyi a ranta a nan barci ya yi awan gaba da'ita maitattare da mugayen mafarkai, kafarta da ake tabawa shi ya farkar da ita ta shiga zazzare idanu ido biyu ta yi da wannan saurayin ya na mata murmushi ya miƙa mata wasu kaya babu musu ta karɓa saboda tana buƙatar canza kaya, fita yayi ya barta ya bar mata wutar Dakin babban daki ne mai tattare da dakuna dakuna ita dai ba ta bi takan dakunan ba ta shige banɗaki ta yi wanka a gaggauce ta fito ta na so ta yi alwala amma ta kasa ta fashe da wani irin kuka saida tayi mai isarta ta goge fuskarta ta fito zaune ta iskeshi ya zuba mata idanu so ta ke ta zazzage shi amma da ta kalleshi wani irin tsoronshi ya ke rufeta, wutar Daƙin ya kashe wani irin iska ya turnuƙe daƙin kafin wani lokaci sai ga su a sararin samaniya suna tafiya runtse idanunta ta yi ta shiga addu'a a cikin ranta wani irin guguwa ya tunkaro su baƙiƙirin. Tsoro ne ya kara mamayeta kafin wani lokaci sai ga su a wani qungurmin da ji amma wannan ya babbanta da sauran, wurgata ya yi ta fadi cikin wasu duwatsu kara ta yi marar sauti saboda azaba muryata baya fita domin yunwa yabi ya cinyeta, a gabanta ya tsaya ya na kare mata kallo zuwa can ya dagata sama da hannunsa wanda ya yi wani irin tsayi nan take kamaninsa suka canza ya koma wani halitta mai soratarwa, "Maryam kin fiye taurin ƙai da kin amince kin karɓeni a matsayin mijinki da kin huta..." Mugu azzalumi wallahi ka ji na rantse ba zan taba karɓeka ba ni Almust... Matseta Yayi da hannunshi ya shiga ga na mata azaba da farccen yatsun shi sai ihu take tana neman agaji, har yanzu ta na saman sai wutsil wutsil ta ke wannan ya zama na ƙarshe da za ki kara kira min sunan wancen banzan lusari marar amfani, zaki ja mishi bala'i Maryam zan ruguza rayuwarsa tunda kinfi son sa a ƙaina. Yana gama maganar shi iska ta yi sama da su sai ga ta a wannan baƙin daƙin wannan karon zafi aka sanya mata a daƙin wani irin zufa ya ke tsatsafo mata daƙin ya yi wani irin tiriri tamkar garwashi aka qunna kuka ta ke sosai tamkar ranta zai fita.
____________

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now