8

1.3K 118 13
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

BABI NA GOMA SHA TARA

*K'AIK'AYI*

PAGE 8

Duk abinda ya faru sai da ya dawo masa sabo, wallahi daya saki juwairiyya ya gwammace ya mutu, bazai samu macen da take da hakuri kamar juwairiyya ba.

Da ciwon kai ya kwana duk da baiyi bacci sosai ba, washe gari koda ya dawo daga masallaci bai shiga bangarenshi ba sai ya wuce bangaren juwairiyya, ya kwankwasa kofar Ahmad ya bude batareda yayi magana ba kawai ya shiga cikin gidan direct dakinta ya wuce ya sameta kwance kan gado tana bacci idonta a rufe amma sun kumbura, takalmin kafarsa ya cire sannan ya kwanta bayanta, ajiyar zuciya ya sauke sai yaji kamar su dauwama a haka, daganan ya rufe idonsa bacci ya dauke shi.

Sai karfe Tara suka tashi itace ta fara tashi motsinta ya tada shi, sai ya mike zaune yana kallonta, saboda bata saba yi masa tsiwa ba sai ta kasa koda yi masa mugun kallo tana cewa "mekake yi anan? Dan Allah ka tashi ka Fita" yawu masu d'aci ya hadiya sannan ya riko hannunta yace "Dan girman Allah kiyi hakuri nasan laifina ne, amma kuma ai na tuba tuntuni, wallahi ko akan waccen yarinyar tsautsayine, daga kanta ban kula wata mace ba inba ke ba, koda tazo da cikin yaron nan nariga na tuba bansan wata mace ba inba keba, tunda kika iya daukar wancen wallahi ko wannan zaki iya na miki alkawarin wallahi duk abinda kikeso Indai bai sabawa Allah ba zan yishi" gabanta ya fadi ganin ya soma yi mata hawaye amma sai ta dake batada buri irin ya fita daga dakin, ta kwace hannunta tana cewa "kafita zan yi tunani dan Allah ka fita" ta fada tana kwace hannunta, baya so ya takurata ta kara birkicewa sai ya mike yana cewa "ki taimakeni da abinci, rabona da naci wani abu tun jiya da rana a gidan Anty asabe" bata amsaba shima bai jira ba ya fita.

Yan gidansu kabir da suka zo ganin gida sun fita da al'ajabi amarya kamar mai ciwo, duk abushe haka gashi batada walwala, da dan tseguminsu suka fita shi kabir din yana jin su amma bai fito ba dan dakin ma rufewa yayi, sai da yaji shuru sun gama fita sannan shima ya fito daga nashi dakin.

Ganinsa kawai tayi tsakiyar palon ta mike da sauri zata gudu ganin kallon dayake mata, ya daka mata tsawa sai ta tsaya kawai tana kallonsa yace "ke zonan" duk inda jikinta yake rawa yake yi, ta matso kusa da shi tana hawaye, tsaki yayi yana cewa "Alkawari ne duk ranar dana ganki koda sau goma ne saina mareki sau goma" yana rufe bakinsa ya kwada mata mari sai da ta daina ji na yan sakanni, koda ta dawo hayyacinta yabar Palon kukan ma yaki zuwa, zama tayi kasa ta buga tagumi, tunani take abinda sukayi da kabir zina ce kuma duk Wanda yayi ya aikata zunubi Allah kuma zai kamashi, kenan ita irin kamun da Allah yayi mata kenan, lallai tayi dana sani ta kuma tafka babban kuskure, ta ina zata bi ta gyaro barnar da tayi batada mafita, ko waya batada shi balle ta kira UMMI, tana zaune wurin har aka kira sallar magrib, dakinta duhu sosai setazo toilet din Palo tayi alwala tayi salla a Palon saboda nan ne keda haske kadan, anan inda tayi salla ta zauna tana istigfari har akayi sallar ishai  tayi, jikin kujera ta Dora kanta bacci yasoma daukarta sai taji alamar shigowar motar kabir, da sauri ta tashi tsaye, Marin daya mata dazu yasa kunnenta ciwo, gudu tayi ta shiga daki tayi karo da center table ta fadi, bata San taji ciwo ba sai da ta shiga dakin taji kafarta na ciwo, kwantawa tayi tana kuka da sauraren yadda cikin ta ke kugi akan yunwa, tunda aka kawo abinci sau daya basu ci ba ba akuma kawowa ba.

Washe gari koda ta tashi kafarta kumbura har tana kyalli, dakyar ta lallaba tayi salla taci gaba da kwanciya, har azahar tana kwance yunwa zata kasheta tana tsoron fita, kota fita ma babu abinda zata girka babu kayan tea sannan ko akwai kayan abinci babu murhun da zata dafa.

Juwairiyya tayi mamakin ganin Hajiya a gidanta, tunda tayi aure Hajiya bata taba zuwa gidan ta ba amma itace yau tazo da kanta, ruwa ta kawo mata da abinci amma hajiyr bata ci ba,ta kalli juwairiyya tace
"Yayar mijinki taje inda nake ta fada min halin da ake ciki, shiyasa na dauko jawahir saboda duk abinda kike kullawa tare kuke yinshi, kuma na rufa miki asirine saboda nasan idan babanku yaji saiya matukar saba miki, haba juwairiyya, ina iliminki da hankalinki suka tafi? Da nayi tunanin saboda kina son Saifullahi kika yi hakurin zama dashi amma kuma yanzu sai ki kara turashi ga halaka? Anji tun farko an miki laifi kuma kinyi hakuri, amma sai ki zubar da ladarki a banza, kaddara ce ta afka kan khadija amma ke kanki kinsan khadija batada wayo, duk irin kullin da Abbansu yake musu sai da ta fito da hanya, amma bazaki dauki laifin duniya ki Dora kan Saifullahi ba, dan ya aikata waccen laifin ai yanzu bashi ya dauko khadija yakaita inda zatayi zina ba dan haka ki sassautawa zuciyarki, ki kira Malam ki fada masa kinjanye maganar saki azo a cire wannan ginin da akayi ki zauna da mijinki lafiya amma fa idan na isa dake" kanta a kasa tace "insha Allahu Hajiya za ayi yadda kikace" batareda Hajiya ta amsa bata ba tace "jawahir idan kin gama tsegumin kizo ki maidani kafin mai gidan ya dawo ya sameni" dariya kadan sukayi dan sunga kokarinta ma da tayi karfin halin zuwa.

Da yamma ta tura Ahmad ya dubo mata ko Abbansu ya dawo, sai gashi ya dawo da gudu yana hawaye yace "ummi Abbanmu yana can palonsa a kasa..." Kafin ya rufe bakinsa ta fita da sauri, jikinsa yayi zafi sosai numfashinsa kamar zai dauke, aljihunsa ta laluba ta dauko key din mota dan ko takalmi bai cire ba daya dawo daga office, Ahmad daya biyo bayanta shi ya kama mata shi suka shiga mota, sai a lokacin ta tuno da ta Dade batayi driving ba amma ta dake, kafin ta samu mai kaisu ai sun wahala.

Kwantar dashi akayi saboda jininsa ya hau sosai ga ulcer dama tuni yanada ulcer shiyasa baya ragawa abinci.

Bayan sati uku khadija na zaune a Palo bayan taji fitar kabir da magriba, taji hayaniya a waje ta kurawa kofar ido taga masu shigowa sai taji ana rangada guda, mata sunfi su ashirin, wata yar matashiya na tsakiyarsu lullube da gyale, suka wuceta dansu basu ma ganta ba, har dakin khadija suka kaita suna cewa "Allah ya kawo kazantar daki ya bada zaman lafiya wasila" wani shuru taji a kanta ta kwanta kan kujera har suka gama fita. Bata iya motsawa daga wurin ba har karfe goma, kabir ya shigo kallo daya yamata ya dauke kai, ta tabbtar da abinda ta gani dazu dan gashi nan acikin babbar Riga.

Dakin da aka kai amarya yayi sallama ya shiga tana zaune kan gado ya bude wardrobe, duk kayan da khadija tayi amfani dasu ya Ciro ya kai palo yace mata, ki kwashe kayanki, ki kaisu dakin can na tsakar gida, kiyi sauri kuma zan rufe kofar zamu kwanta nida amaryata.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now