Shafi na uku

2.2K 220 0
                                    

KUNDIN HASKE

            Al K'ALUMAN Marubatan HASKE

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
  MAMAN KHADY

ABOKIYAR ZAMA
(Kishiya)


BABI NA HUDU

Shafi na uku


Zaune suke gaba d'ayan su a falo suna hira, Abdallah ya kalli bilkisu cikin k'asa da murya yace "please uwargida dan Allah ki tausayamin wallahi kwanakin da kika bani sunyi min yawa."

Saurin kallon b'angaren da aysha take tayi sai taga hankalinta nakan yara suna wasan su, wata harara ta wurgamishi kamin tace "Dan girman Allah kabari Abba wallahi zaka bata zaman lafiyan da muke ciki."

Shima harararta yayi kamin yace "Ke nifa wallahi da gaske nake in banda zalinci wane irin karin kwanaki zaki min akan wanda shari'a tabani iye..?!"

Kallon ta aysha tayi tace "Aunty bari in d'an shiga ciki tunda dai yaranki sun d'auke hankalinki yau ko kulani ba kiyi ko?"

Cike da kunya asyhar tace "Wallahi shirmen farouk ne ya d'auke min hankali amma kiyi hakuri, kumama aiga abba nan kusa dan dai naga kamar yau fishi yake yi ne."

  Da yake haka suke k'iran Abdallah da suna abba sabida yaran, ita kuma bilkisu saita k'ira aysha da suna aunty dan yaran su saba da fad'a.

Bilkisu na barin wajen shima ya bita tsabar rikicin da yake fama dashi.

Kafad'unta ya rika da karfi kamin yace "Bilkisu kada mufara haka dake fa, wai me yasa zakimin haka ne? wallahi tun lokacin da kikace kin k'aramin kwanaki nai tunanin wasa kike yi dan me zakimin haka?"

Kwace hannuwanta tayi kamin tace "Si dama nasan zaka biyoni sabida banso tasan maganar me muke yi yanzu, sabida Allah so kakeyi idan taji tai tunanin cewa gajiya da ita kayi? haba mana duka yaufa kwana tara dan Allah kabari ka idasa ni wallahi bacinma wani tunani da nayi da wata d'aya zan baka yanda zaku fahimci junanku sosai."

Tsabar takaici daya kamashi bar mata d'akin yayi kawai yana jan tsaki.

Mutmushi tayi kamin tace "Allah saika k'arasasu nima kamin nan na huta sosai har gyarama nayi maka yadda babu raini bare wulakanci tsakaninmu."

Kwanciyarta tayi tana jiran bacci ya d'auke ta. Koda yake ofis ma kasa hakura yayi shi kam sosai yarasa jarabar data sameshi aysha na matukar k'ok'ari dashi domin tunda aka kawota betab'a d'aga mata k'afa ba koda na kwana d'aya ne kuma yana gamsuwa da ita sai dai tsabar sabon da yayi da bilkisun da kuma yanayin yanda take tafiyar dashi shine ke kuma tayar mishi da hankali kwanakin da yayi be kusance taba jinshi yake kamar marayan daya rasa iyayen sa lokaci d'aya.

"Hello baby billyna ya kike?"

Murmushi tayi kamin tace "Ah me gidan mu ya aikin naka?"

"Lafiya lau, nine dai ba lafiya ba tawan kiji tausayina dan Allah wallahi na gaji haka."

"Dan Allah kaima kayi hakuri amma insha Allah saika idasa kwanakinka garama ka hakura idan ba haka ba kuma in had'aka da amarya nan wajan tama ka daina samu."

Yace "Zakiyi mamakin yanda zan yagalgalaki wallahi matukar kika shigo hannuna duk sai na rama."

Dariya tayi sosai bayan ya kashe wayar, 'Alhamdulillah. Ta furta lokacin da ta tuno yanda hankalinta yake kwance yanzu inda ta biyema zuciyarta aik'ila da yanzu tana gaban iyayenta da saki d'aya ko biyu.

GIDAN ABBAKAR    
   Salma da kawarta suna hira "Ke wai suwaiba dama haka kishiya take? ashe kishiya masifa ce? wallahi Allah ya isa tsakanina da Abbakar kuma insha Allahu shima sai anyima d'iyarshi kishiya tunda yayomin ita.

Dariya suwaiba tayi kamin tace "Dubeki da wata banzar addu'a, ina ce kema d'iyar kice idan ma anyi mata kishiyar? ai tunda kika bari ta shhigo to wallahi sai dai hakuri amma kishiya ko bala'i balle naga taki wayayya da ita wallahi."

Tsaki taja kamin tace "Uhmm! wallahi bakiga yanda yake nan-nan da itaba niko ai ko magana banyi mishi kuma ban yadda ta tab'a min yara ba gata da son kuma da shegen son yara.

"Ah toh ni dai wallahi tuna miki zanyi kishiya ba abokiyar zama bace, kuma baka sakin jiki da ita ni dai na gaya miki."

Cewar suwaiba tana gyara hijab d'inta. (Allah kai mana tsari da k'awaye irinsu suwaiba Amin).

Yoo ba dole ya shareki ba salma mutun yana mijinki amma kina gaba dashi, yo ko beyi amarya ba ai kina cikin matsala balle kuma yayo sabon aure.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now