8

206 12 2
                                    

*KUNDIN HASKE*💡

*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

    *ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

    *NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)

                        *8 Ƙarshe*

Bai wani tsaya ba ta lokaci  ya wanka masa wani zazzafan  mari sai da ya ga wasu taurari, kafin ya dawo haiyacinshi ya kara mishi wani. ya shaƙesa nan ya shiga dukansa ta ko ina, don ub**ka matar tawa za ka riƙe? Kai dakiƙin ina ne? Saɓar iskanci da tambada a garin mai tsarkin ma sai kun nuna ku ƴan iska ne? Dama na jima  ina  jin ana  cewa ku larabawa duk ya wancinku ƴan banza ne baku da aiki sai lalata ƴaƴan mutane, musamman yaran yaran da su ke muku aiki. To Bara ka ji ita wannan ta fi ƙarfin ub**ka ba kai ba. Ɗaga jin irin maganganun da Almustapha ya ke za ka fahimci ya fita hayacinsa banda dukan wannan yaron babu abinda ya ke. Ganin Almustapha zai yi ki san kai Maryam ta shiga ihu ta na neman ceto da kyar aka rabasu ya kunkuduma ma mutumin ashar sai fadi ya ke su kyalesa ya kashe ɗan iska mai bin matan mutane. Shi dai mutumin sai ihu ya ke ya na kuka da saboda ba karamin duka ya sha ba, hancinsa na zubar da jini ana rabasu ya bar wajen da sauri. Almustapha ya ja hannun Maryam su ka nufi mota ma'aikatan gidan suka kai musu kayansu sun saka a bayan but y adauko kuɗi masu yawa ya wasa musu ya ja motar da saurayi, Balarabe da bakar zuciya su na shirin bin motarsu wasu yan sanda da su ke gefe suka basu hakuri da kyar su ka hakura da yunkurinsu sai sun daure Almustapha su ga ub**da zai hito da shi.

Su na iska hotel ɗin ya tura ta cikin daki ya hadata da bango ta tsorata sosai saboda duk kamaninsa sun canza idanunshi sun janjawur tamkar garwashin wuta. Cikin kakausar murya ya ce, "Uba** me ki ka tsaya yi da wani kato da aurena ankanki?" Hawaye ya shiga zubo daga idonta ta na so ta yi magana tsoro ya hanata, ganin yadda ta tsorata ya ja baya kadan ya fada saman gado ya na sauke ajiyar zuciya. Shi ka dai ya san me ya ke ji son yarinyar nan zai ƙashe shi, Hamdallah Maryam ta kawo mishi ruwa mai sanyi bai yi musu ba ya amsa ya sha ya sauke ajiyar zuciya, ya janyo ta jikinsa ya shafa bayanta ya na cewa, "Ki yi hakuri Darling na ka sa saita kaina ne kishinki ya rufe min ido, don Allah kada ki sake min irin haka ina mugun sonki sonda Ni kaina ban san iyakar shi ba, ki ce mahaɗin rayuwata komai nawa naki ne Maryam."

Ya dauko wani ɗan karanmin akwati cikin jakarsa ya buɗe sai ga wani haddadan sarka ta azurfa tareda yan ƙunnayensu ya mika mata a hannunta ya ce, "Maryam wannan sarkar naki ne tun ranarda aka kawoki gidana na ajiye miki shi kasancewa wani Ɓoyayyen Sirri ya shiga cikin lamurranmu ban samu damar baki shi sai a yau, karamar kyauta ce ɗaga gareni Sakamakon budurcinki da kika mallaka min, ba zan iya biyanki ba Maryam koda duk dukiyata na baki, sai dai zan kwatanta faranta miki har ƙarshen rayuwata In shaa Allah." Farinciki murna su ne suka mamaye Maryam ta rasa me za ta ce mishi kawai ta rungume shi ta na kising dinshi a ko ina zuwa can ta dakata ta ce "Mijina ka cire shaku a kaina ka amince dani ka bani duk yardarka, Ni Maryam ba zan taba cin amanarka ko na ci zarafin aurenka da ya ke kaina, nan ta sanar dashi duk abinda ya wakana tsakaninta da mutumin ba abinda ya ke tunani ba ne. ta cigaba da cewa a yadda na ke sonka bakina ba zai iya furta maka saboda duk inda zan ajiyeka ka wuce nan, kuma Ni bana son ka bani kyautar komai sai abu ɗaya..."

Cikin zumudi ya ce "Ina jinki ki fadi koma meye idan har bai sabama shari'ar Musulunci zan miki shi."

Ta yi murmushi ta ce, "So na ke ka cigaba da kasancewa tare dani har ƙarshen rayuwarmu. Ka ɗauke idanunka ka duk wata ƴa mace Ni kuma idan ka min haka ka gama min komai zan yi matuƙar farinciki."

Murmushi ne ya suɓuce masa ya ce, "In shaa Allah kada ki damu ke ɗin nan kin isheni rayuwata fatana Allah ya bamu zuri'a masu albarka ameen, amma ki ƙarbi wannan kyautar don Allah Darling." Ta amsa ta ajiye daga nan suka lula wata duniyar ta daban wanda ma'aurata kawai su ke zuwa can."

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now