Shafi na uku

1.6K 139 1
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


3




Duk yanda Fatima ta so hana Husnah su je gidan warce ta kira da kawarta kin saurarenta tayi haka ta tilastata sai da suka hau mota suka dau hanyar gidan kawarta da suka hadu da a IG me suna Sadiya, Allah ya so ta fito da kudin da Umar ya bata daxu da safe, Tafiyar kusan minti talatin da wani abu suka yi kusa da cikin garin Abuja kafin su iso gidan, sun dade bakin gate don sai da mai gadi yaje ya sanar da xuwansu kafin su shiga gidan, tunda Fatima taga irin kallon da yan gidan ke ma Husnah jikinta yyi sanyi kana gani kasan sun gaji da xuwanta, Sadiyar ma sama sama ta kula su bayan ta fito  kafin ta kawo masu ruwa da kayan flour, tuni Husnah ta sauka kasa ta fara cin abubuwan dake gabansu, Fatima ta ki cin komai don duk ranta ya gama baci, Sadiya dai na xaune tana kallo a Tv don duk yan gidan da suka tarar a parlor sun bar parlorn, Husnah ta cika baki da cake ta ce "Kawata mun xo neman wata alfarma ne gun ki don Allah...." Sadiya ta kalleta tace "Toh ina ji" Husnah ta kora cake din da drink ta mike tace "Toh ina xa mu je muyi maganan?" Tashi Sadiya tayi ta fita balcony Husnah ta bi ta tana kashe ma Fatima da ta hade rai ido, bayan sun fita nan ta gaya mata abinda yasa suka xo, har da risinawarta tana roko, Sadiya da ta d'an yi jim tace "Har da kaya?" Husnah tace "Hoto kawai xata yi wallahi" Sadiya tace "Shkkn ba matsala" amma kana jin ynda tayi furucin kasan takaici ne ya isheta, dakin mai aikinsu ta kai su, Husnah na rike da hannun fatima da taki sake fuska tana bin ko ina na dakin da kallo tana cewa maa sha Allah, Allah ka bamu irin haka, suna ta xaune dakin sai ga Sadiyar ta shigo da kaya hannunta da abun kwalliya, nan ta mika ma Fatima kaya na Riga da skirt da kayan kwalliya da mayafi, ta juya xata fita Husnah tace "Ki yi hakuri ki d'an ara mana wayar ki xai fi kyan hoton kuma xa mu yi wasu a nan" Sadiyar ta kalleta sannan ta xauna dakin tace "Toh idan kun gama sai in mata"  har Husnah ta gama yi ma Fatima kwalliyar kallonsu Sadiya take, a xuciyarta kuma addu'ar shiriya da Allah ya raba su da karya take barin Fatima da ta yi mata kyau sosai, ba laifi Husnah ta iya make up sosai don ba karamin kyau Fatima tayi ba duk da bata yrda ta cika mata kwalliyar ba, Sai washe baki Husnah take ganin yanda ta fito da kawartata, ta juya ta kalli Sadiya tace "Toh dauketa hoton kawata" nan Sadiya ta mike don daukar Fatima hoton, sosai Fatima tayi mata kyau sai dai taki sakin fuska, kusan biyar ta dauketa a daki, Husnah tace "To ya isa haka mu je waje" tana rike da hannun fatima suka fito compound, nan ma sadiya ta dinga mata  hotunan, Husnah na nuna masu background, sae jaraba take wai fatima ta tsaya dososo taki murmushi, Fatima ta galla mata harara tace "Ke kar fa ki dameni wannan din da nake fa, ni na ma gaji ki rabu dani" ba shiri Husnah ta ja bakinta tayi shiru, Sadiya dake ta kallonsu ta d'an yi murmushi tace "Toh wannan na karshen dai ki daure ko dariya kiyi xae yi kyau sosai" Fatima bata san lkcn da tayi dariyar ba a haka Sadiya ta dauketa Wanda duk hotunan babu Wanda ya kai sa kyau, Husnah sae murna take, a nan kuma aka gama daukar hotunan suka koma ciki Sadiya ta tura masu duk hotunan a wayar Fatima,  Fatima ta mayar da kayanta ta linke na Sadiya ta ajiye tana kallonta tace "Sister nagode sosai" Sadiya tace "A'a ki tafi da su na bar maki" nan Husnah ta canxa fuska sae dae bata ce komai ba, sai da suka tashi tafiya tace "To ni baki bani kayan ba Sadiya ko na maki wani laifi ne" Sadiya ta yi murmushi tace "Bari in dubo maki to" daga haka ta tafi dakinta ta dauko mata wani kayan ta bata, Husnah ta dinga godiya har da durkusawa tana washe baki, Fatima da takaici ya isheta ta fice daga dakin suna biye da ita, a bakin gate Sadiya ta basu dubu daya kudin mota Fatima ta mata godiya ta fita ta bar Husnah dake ta godiya kamar wata marokiya ta dau hanyar titi, da gudu Husnah ta kamota tace "Kinga masu kirki koh, kuma ace duk sati baxan dinga xuwa nan ba, ko don irin cimarsu ni bbu Wanda ya isa ya hanani xuwa wllh" Fatima dai bata tanka ta ba har suka shiga mota xa su koma Suleja. Sai kusan karfe biyar da rabi suka isa gidansu Husnah, Fatima da duk hankalinta ya gama tashi tace "Kinga baxan shiga ba xan samu adaidaita daga nan in wuce gida nasan Ammi na can tana jirana na dde sosai, sai mun yi waya" Husnah ta rikota tace "Toh amma banda masa bakar magana plss, ki kara editing hotunan ki tura masa masu shegen kyan ciki plsss ki rufa mana asiri mu ma mu faso gari kwanan nan" Fatima tace "Naji ni dai sai mun yi waya" daga haka ta wuce da sauri ba tare da ta damu da dubu dayan da aka basu da Husnah ta boye a jaka tun daxu ba, adaidaita ta samu ya kaita har kofar gida, Ammi dake tuka tuwo tana xaune kan kujera kusa da coal pot bata ko amsa sallamarta ba, a sanyaye ta durkusa nesa da ita tace "Don Allah don annabi Ammi kiyi hakuri nasan na dde sosai, kinga dambu tace in tsaya in koya mata bata iya ba kuma shi xata yi, shine kawai na tsaya na girka mata, kiyi hakuri Ammina" Ammi ta kalleta tace "Toh ni na ce maki wani abu ne Fatima" Fatima tayi shiru bata ce komai ba, Bude ledan da ta shigo da tayi ta fiddo kayan ciki da mayafi tace "Gashi Ammi ta bani, nace ta bari na gode amma ta ki saurarana" Ammi tace "Allah ya saka da alkhairi" Fatima ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Ameen" sannan ta mike ta shiga cikin dakinsu tana murmushi. Ita ta karasa sauran aikin gidan Ummi na taya ta, suna gamawa ta daura ruwan wanka ta koma daki, sae kusan shidda ta fito tayi wankan ta daura alwala ta shiga daki, Ta gama shafe shafenta ta saka doguwar riga ta dau wayarta ta hau saman gado ta bude data, IG ta shiga ta duba DM dinsu da Elbash taga har lkcn bai ce komai ba, ta d'an yi jim, sai kuma ta tura masa "Are you ready to listen to why I followed you and went ahead to ping you?" Daga haka ta fita ta koma WhatsApp, sai da taji kiran sllh ta kashe data ta mike, tana idar da sllh tayi azkar dinta sannan ta fita xuwa dakin Ammi, Ammi dake xaune Da Ummi da Yusuf suna cin abinci ta kalleta, xaunawa tayi gefen Ummi, Ammi dai bata ce mata komai ba tana jiran ta ji me ya kawota sanin bata shigowa sae idan abu ya kawota, Ita kanta she was uncomfortable can kuma ta mike xatah fita Ammi tace "Kin ci abincin ne?" Fatima ta kalleta tace "Shi xan je in ci ynxu" Ammi dai bata ce mata komai ba har ta fita, ta rasa irin yar tata, bata taba ganin yar da ke kin sakewa da uwarta kamar Fatima ba, Fatima ta debi tuwo kadan da miyar kubewa ta saka cokali ta wuce daki, har ranta ta tsani cin tuwo, ta gama jagwalgwa shi ta tura gefe ta dau wayarta ta bude datan ta, message din Elbash ta gani yace "I am not interested" tsuru tayi tana kallon message din, can tayi murmushi tace "is that so??" ya bude message din yaki cewa komai, bayan kusan minti sha biyar tace "u knw something I already knew about you even before chatting u up?" bayan wani lkci yace "That's ur cup of tea..."

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now