5

1.7K 134 11
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*K'UNGIYAR HASKE WRITER'S ASSOCIATED*
(Home of expert & perfect writer's).

*Tare da*
    *Alk'alamin*

*MARYAM IBRAHEEM*
(Ummu Hanan).

*BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

*SATAR FITA*
     (Halayyar wasu matan).

*SHAFI NA BIYAR*

Rabi'a dai ynx ba damar fita saboda yadda laulayi ya taso ta gaba kullum batada cikakkiyar lafiya,hakan yasa duk wani yawo nata ta ajiyeshi gefe guda.

    Ita kanta yarinyar tata dad'i take ji saboda kullum tana tareda mamanta ba kamar lokutan baya ba da kusan kullum saidai ta kaita gidansu waleed ita tayi ficewarta.

    Sosai Ahmad ke kula da ita da biyewa duk wasu tsarabe tsarabe irin na masu juna biyu shidai fatanshi ubangiji ya sauketa lafiya ya k'ara ganin k'wanshi a duniya.

   ***
Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa da dad'i ba dad'i yayin da cikin Rabi'a keda wata uku da y'an satanni, ba laifi laulayin yayi mata sauki saidai d'an abinda ba'a rasa ba wannan kuwa duk mai ciki bata rabo dashi har sai ranar da aka rabu lpy,(fatanmu ubangiji yayiwa yaranmu albarka yasa bamuyi wahalar banza ba ya k'ara shirya manasu kan tafarki madaidaici👏🏻👏🏻).

        * ......*
Kwance take bisa doguwar kujera a falonta,bayan fitar Ahmad d'in, sai faman tand'ar baki take tana shan tabar malam dan tunda ta samu cikin nan kusan kullum saita shata take jin dad'i, kasancewar asabar ce ba makaranta husna na gida tana gefen ta a xaune tana yiwa y'ar babynta kitso a cewarta🤣.

   Wayarta dake kusa da ita tayi k'ara alamun neman d'auki, hannu takai ta janyo wayar tana duba mai kiran nata, sunan bushra ta gani yana yawo bisa screen d'in wayar.

    "Yau a gari".
Ta fad'a tana kokarin yin picking dan kwana biyu sun rabu da had'uwa da ita.

   Sallama tayi suka gaisa, bushran tace

   "Oh k'awata saduwa tayi wahala tunda kika samu cikin nan".

   "Bari kawai aminiyar wnn cikin ai yana bani wuya kullum ba lpy amma ynx alhmdllh da sauki sosai".

    "Toh Allah dai ya raba lpy".

   "Amin" Rabi'an ta amsa mata.

   Shiru sukayi kafin bushran tace

   "Am...dama dai wata fitace ta taso gobe amma kekam nasan bazaki samu zuwa ba tunda ga halin da kike ciki".

   Kwanciyarta ta gyara tana tambayar ta inda za'aje.

   "Ai nake gaya miki bikine na masu dashi, Ina wannan k'awar tawa danake baki lbrn ta ta rijiyar zaki...?"

   "K'warai kuwa kina bani lbrn ta". Rabi'an ta amsa mata.

   "To in gaya miki bikin k'anin mijinta ne ya taso ta gayyaceni gobe yini shine nima nace bari in fad'a miki muje tare dan akwai gwangwajewa nake gaya miki bikin manya ne".

    Zaune Rabi'a ta tashi tana fad'in

"Aikuwa aminiyar ba za'ayi bada niba sai naje na kashe kwarkwatar idona ki jirani goben kawai mu fasa".

Dariya bushran tayi tace

   "Shegiya anji yawo ko..?"

   "Ah to keya kika gani ba gara muje mu ganewa idanunba da abaka lbr gara ka bayar koya kikace...?"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now