Shafi na shida

1.9K 189 16
                                    

KUNDIN HASKE

AL-KALUMAN MARUBUTA...

NA KUNGIYAR...
     HASKE WRITERS ASSO

TARE DA AL-K'ALAMIN...

HAFSAT RANO

WAYAR MIJI

Babi na takwas

Shafi na shida

Kukan ta ya karad'e baki d'aya harabar wajen, cike da tausaya wa kowa ke kallon, tsaye take a kofar wajen bayan likita yace ta d'an jirasu a waje, bata san in da zata sa kanta ba, sai kawai ta hango Jabeer yana takowa kan barandar da alamun ita yake nema. Ganin kiran nata yayi yawa yasa yayi tunanin komawa gida ko akwai wani abu, be sameta ba sai matar Malam Hassan ce ta aiko yaranta ya gaya masa bata nan ta tafi kai Mashkoor asibiti, kafin ta tafi asibitin dama sai data shiga gidan anan ma ta ari kudin kati da d'an sahun da zai kaita.   Sai ya juya da azama ya nufi asibitin, direct Emergency Unit yayi don yasan dole a chan zai tarar da ita.

Da sauri ta isa gabansa ta ruk'unkume shi tana kuka,

"Kiyi shiru ki fad'a min me yake faruwa, me ya sami Mashkoor." Ya tambaye ta cikin rud'ani da tashin hankali

"Mashkoor ya mutu Jabeer."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya shiga furta wa yana ja da baya hannunsa cikin nata har ya dangana dasu jikin karfen dake kan barandar. Kuka ta cigaba da yi a fili shi kuma yana na zuci, suna nan a haka an rasa me lallashin wani Nurse ta fito, da sauri suka karasa wajen ta da suka lura da alamun magana take son yi dasu. Cikin d'akin ta koma suka rufa mata baya, akan dan karamin gado suka hangi Mashkoor.

" Yaronku be mutu ba..." Muryar Dr ta daki kunnensu.

"Alhamdulillah." Suka hada baki cikin madaukakin farin ciki.

"Kawai dai dogon suma yayi, wanda tsananin galabaitar da yayi ne ya jawo hakan, yanzu dai an baku gado zuwa a ga jikin nashi. Sai a kiyaye gaba da zarar yaro ya nuna yar alama ta rashin lafiya ayi kokarin kawo shi asibiti."

"In sha Allah Dr, mun gode."

Fita sukayi Jabeer ya wuce ya biya kudin d'akin da magunguna.

Jinyar Mashkoor shine ya k'ara ladabtar da Khairat, tayi laushi tubus har ta shiga neman shiri da Jabeer ganin yadda yake shash-shareta, hankalinsa kachokam yana kan kula da d'ansa.

Tayi nadamar irin tijarar da tayi wa mijinta, a yanzu kam ta saduda ta tattara duk wasu makaman yak'in data d'auka tayi watsi dasu. Ana haka Mashkoor ya warware sosai, aka sallame su sukayo gida, sai Jabeer ya tsiri cin magani da fuskewa, duk don ya riga yayi wa kansa alkawarin daina sakar mata fuska tun da dai ita bata san mutunci ba, abu ya hadu yayi wa Khairat yawa, ido rufe take neman shiri da mijinta ko ta wacce hanya. Gashi d'an mutuncin nata da yake gani ya gama zubewa tatas.

Duk yadda taso ta shawo kansa abu ya faskara, hausawa sunce "Icce tun yana d'anye ake tank'wara ce." Kuma shi *Yak'i d'an zamba ne"
Ganin wankin hula na neman kaita dare ya sata lalub'o number Anty Maijidda don ta d'ora ta a hanya.  Bayan ta gama karanta mata duk abinda ya faru da irin cin kashin da tayi masa, sai ta rufe ta da fad'a cikin fushi.

"Wannan sam ba tarbiyyar da muka baki bace Khairat, bansan in da kika koyo wannan bak'in kishin naki ba, banda kema dai ina ke ina duba wayar sa? Wanna tsautsayi  ne ya kaiki? Kullum fadan da ake yiwa mata kenan amma na rasa gane wannan musibar, ki barshi yaje chan ya karata da wayar sa, tun da ko kin hanashi na hanuwa zai ba.
Sannan ni haka kika ga muna zaune da abokiyar zamana? Ko kuma haka kika ga su Innani da Yakolo suna yi? Mene ne a ciki don mijinki na neman kara aure, kibi ki tada masa hankali, toh wallahi in zaki nutsu ki dawo kan turba ta gaskiya ki dawo. Ki gode wa Allah ma mijinki aure yake son k'arawa be je waje yana binsu ba, ki nutsu ki jawo mijinki a jiki kafin ki gama fitar masa a rai. Yazo a gabanki yana yin abubuwa don ya kona miki rai. Kinji na gaya miki."

KUNDIN HASKE💡Donde viven las historias. Descúbrelo ahora