8

1K 107 8
                                    

*KUNDIN HASKE*

   *Al-K'aluman* *Marubuta*

    KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

       *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

   *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN......*

      _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu* 🖊

       
               0⃣8⃣

Sati biyu kenan da saka ranan auren su Ruk'ayyah da Nadeeya wanda za'ayi alokaci guda hakan yasa dukkanin b'angarorin ke cikin shiri baji bagani , yayinda ummah ta dage da gyaran jikin yaranta da temakon qanwarta datazo daga sokoto wacce suke kira anty Talatu,dama ita harkantane gyaran jikin amare cikin lokaci guda ko Amaren suka fara canzawa musamman Nadeeya wacce take acike batasa wani damuwa arantaba inka d'auke na halin da qanwarta Ruk'ayyah ke ciki , domin Ruky tarame sosai sbd takasa cire soyayyan Ahmad aranta , Kaman yadda tsanan kamal Alqasim  ke sake samun guri acikin zuciyanta , tun ranan daya kirata takashe wayanta bata sake kunna wayan ba Nadeeya tayi ban hakurin amma babu sauyi , koda Anty talatu ta iso babu irin hakury da rarrashin dabatayi wa Ruk'ayya ba amma abanza , duk da cewa itama d'in tana takaicin yadda kwad'ayi ya rufe idanun yayarta take kok'arin jefa kyakykyawar d'iyanta cikin wani hali nadaban, taji tausayin yadda aka raba Ruk'ayya da nagartaccen yaro kaman Ahmad , sai dai bakin alk'ami yabushe tunda har komi yai nisa basu da ikon hana iyayen su Ruk'ayya aiwatar da ikon su akan yaransu , kaman yadda dangin Abba suka zuba masa idanu hakana umman ma suka kawo idanu suka sa mata , fatansu bai wuce Allah yaraba yaran daga fuskantan wulak'anci a gdn auren nasu ba ,

Ranan daya rage saura sati biyu biki aka kawo lefen Ruk'ayyah , wanda ya girgiza zukatan family d'insu Ruky domin akwatuna ne aka zubesu set biyar nagani nafad'a bama ta akwatunan ake ba tamkar irin yadda aka narka dukiya gurin tsara kayan dake ciki wanda alqalamina bazai iya misalta tsada da yawan kayan dake cikin wad'annan akwatuna ba kud'in d'inki kanshi miliyan d'aya aka sako wanda aka cira naira budu d'ari biyar aka bada tukuicin kayan

Washegary aka kawo na Nadeeya itama akwatuna set hud'u wanda aka zuba kaya masu asalin kyau da tsada , duk wanda yaga kayan da aka kawo na lefen su Ruk'ayyah yasan tabbas yaran gdn arzik'i zasu shiga ,k'awaye da dangi nata zuwa kallon kaya masu hassada nayi masu fatan alkhairy nayi haka dai shirin biki yaci gaba wakana , harkuma zuwa lokacin Kamal Alqasim baisamu dawowa ba k'asan, domin ayyukan dayaje gudanarwa bai gamaba kumashi mutum ne mai bada muhimmanci akan duk abnd yashafi harkokin business d'insa , musamman wannan zuwan daya zama sabon company ne zasu bud'e nayin takalman maza da mata hakan yasa bazai dawoba sai yayi settling komi daya dace

*******
Yau bikin yarage saura kwanaki goma kenan duk wani shirin biki natafiya yadda ake buk'ata amare nacigaba da samun kwakykyawan shiri da gyara daga anty Talatu , Nadeeya itake gabatar da duk wani shiri itada qawayenta domin ko kad'an Ruk'ayyah taba shiga duk wani sabga sai Zainab Zubairu da Aysha Sani ne kawai aminanta biyu da suka taso tare suke gabatar da shiri ta b'angaren Ruk'ayyah , sosai Kamal yasa umar yasakin musu kud'in dazasuyi duk wani harkoki , ta account d'in Aysha sani yaturo musu naira miliyan d'aya da rabi itadai Ruk'ayyah 'yar kallo ce domin duk yadda zasu zauna suna tsara abubuwansu baxaka tab'a jin bakinta aciki ba , kullum cikin kai kukanta ga Allah take akan yabata ikon yin dangana , haushi da wani ciwo takeji a kullum kwanan duniya idn ta tuna da wanine daban za'a d'aura mata aure bada masoyin ta Ahmad ba , wanda yayima garin kano k'aura domin zuciyansa bazata iya juran ganin bak'ar ranan da zaizo ya riskesa ba na auren Kamal da Ruk'ayyah

Misalin karfe takwas na dare Ruk'ayyah da Nadeeya ce zaune bisa katifarsu , can daga tsakiya Zee Zubairu ce ke shirya kayan Ruk'ayyah da aka kawo d'inkunan su daga kd , wanda Ashanty Sani ce takai can d'in sosai d'inkunan suka bada ma'ana domin telan yasan aikinsa , sai da tagama rufe akwatin ne ta dubi Ruky daketa zabga mata harara tana fad'in

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now