3

1.9K 170 21
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        Al’kaluman marubata

   KUNGIYAR:-
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(home of expert and perfect writers)

*TARE DA AL KALAMIN*

*ZEE YABOUR*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

   ......MABUD'IN WAHALA

*03*

     Bayan sallah isha'i, Ya Nura ya kira Sameerah yace gashi nan zuwa, Sabulu ta d'auka ta fita bakin k'ofar su ta wanke fuska, Ta koma cikin d'aki, Ta shafa cream ta murza hoda, Gogaggen hijab d'inta dake k'asan akwati ta d'auka ta saka, Tana fesa turare kiransa ya shigo, wanda hakan ke tabbatar mata da zuwan sa.

    Bata d'auka ba, Ta fito ta kalli Mahaifiyarta dake zaune a tsakar gida tare da k'annen ta suna shan iska saboda yanayin garin na zafi, babu wutar NEPA,

     "Umma zance gun Ya Nurah", " A dawo lafiya, ki kula da kanki, Allah ya tsare ki", Ta amsa da "Amin", Ko da yaushe addu'ar da take mata kenan"

    Saman mashin d'insa Honda wanda ake kira da ladies ta tarar dashi, Tasha yadinsa toyobo, da hula a kansa, Sun matuk'ar yi mishi kyau, Yayin da jikinsa ke fitar da k'amshi mai dad'i,

     Fuskar sa d'auke da far'a yace "Gimbiyata", " Ina wuni?", "Lafiya lau, Yasu Umma?", " Tana lafiya", "Mashaa Allah",

   Mashin d'in sa ya jawo ya rab'a sa da bangon gidansu, Ya zauna kan dakali, ta zauna a gefen sa, Bakin gidansu a lungu yake, mutane basa wucewa ta wurin.

      " Ni fah na k'osa ki zama Amaryata, yaushe zan aiko asa mana rana", Wasa ta shiga yi da yan' yatsun ta cike da kunya, Kunyar ta ba k'aramin burge shi take ba, Ya nisa yace "Gimbiyata da gaske nake, kinga kin gama makaranta", Ba tare da ta d'ago kai ba tace " Zan sanar da Umma ta fad'awa Abba", "Da nayi farin ciki sosai", Tayi dariya, "Ranar da Allah yasa kika zama matata sai nayi sadaka na godiya ga ubangiji", Hannu tasa ta rufe fuska tace " Kai Ya Nura", "Allah da gaske nake, Ni dai Allah na sona da ya had'ani da saliha, kamilar mace", " Nima ina gode ma Allah da ya had'ani da kai", Ta fad'a cike da kunya,

     Hasken fitilar mota ne ya dalle musu ido, Nurah ya saka hannu yana karewa, Yayin da Sameerah ta kawar da kai gefe,

     Motar tayi parking saitin su, tare da kashe fitila, Dalleliyar mota ce wacce kallo d'aya zaka mata kasan mallakin ta naira ta zauna mishi.

    Ya Nurah cike da tsoro da fargabar Allah yasa ba wani ke son mishi k'wacen Sameeran sa ba, Fuska d'auke da damuwa ya kalleta "Waye wannan?", Kafin ta bashi amsa Rahma ta fito tana ta zuba k'amshin turare mai k'arfi, ta yafa k'aramin gyale, Ko kallo basu isheta ba, Ta nufi motar ta bud'e murfin gaba ta shiga.

     "Me zai hana ki rik'a ba yar' uwar ki shawara", Tayi murmushi mai cike da takaici tace " Ina lurar da ita, bata d'auka dai", "Allah ya shiryar da ita", " Amin", Suka cigaba da hirar su ta masoya.

     "My baby My baby!", Cewar Lukman, Tayi fari da ido tace " My Hubby, Ya hanya?", "Hanya kamar wanda yayi tafiya mai nisa", " Uhm to ya lafiyar ka?", "Lafiya nake babyna", " Ya mutan gida?", "Lafiya, suna gaisheki, ga sak'o ma Mummy tace a kawo miki", Ya jawo leda gefensa ya mik'a mata, Ta karb'e tana fad'in " Aiko nagode, ka mata godiya", "Ga number ta ki kirata", Ya karantu mata number, ta rubuta tayi saving da Mummyna(Kuji zak'ewa😂)

     " Ni zan koma tara tayi", Ya Nurah ya fad'a yana duba agogo, baya tab'a kai dare sosai a wurin ta, Hasalima bai cika dad'ewa suna zance ba, a cewar sa idan Namiji da mace suka keb'e na ukun su shaid'an ne, Yana k'ok'arin kiyaye duk abunda zai jefa su halaka, "Allah ya kai ka gida lafiya, A gaida su Inna", " Amin zasu ji",

   Ya hau babur d'in sa, Yana tashin sa yak'i tashi, Ya shiga yi masa dabura amma a banza, Sameerah cike da damuwa tace "Ko zaka kira mai gyara", Wayar sa ya d'auka ya kira mai gyaran, yace yana zuwa.

    Rahma na kallon su ta cikin mota tana dariya, " Wai fah wannan shi zata aura, Mutum matsiyaci futik mashin d'in ma da k'yar ake tashin sa", Lukman yace "So ba ruwan shi ai, ita a haka take son shi", " Tabb bazan iya auren gaja ba", Ya girgiza kai ya janyo wata hira akan turo iyayensa a saka rana, baya so a d'auki lokaci, Rahma kamar ta fasa ihu jin zai turo iyayen sa.

    Cikin minti 15 mai gyara yazo, Ya kwance mashin ya duba, Yana basa wuta ya tashi, Nurah ya tambaye sa "Nawa ne kud'in gyara?", Yace " D'ari biyar", Ya laluba aljihun sa, ya zaro d'ari biyu ita kad'ai ce dashi "Ga wannan kayi hak'uri, gobe ka sameni shagona ka karb'a", Mai gyara ya had'e rai yace " Mallam bazan yarda da haka ba", "Haba Nafi'u kamar yau ka saba mun gyara", Cikin d'aga murya yace " Kaga Mallam ka nemo kud'ina kawai ka bani yanzu",

Cike da mamaki Nurah ya bisa da kallo, yasan akwai mutunci tsakanin su, Nafi'u da biyu yayi, ganin motar Lukman yayi haka dan ya fito ya  bashi kud'i,

   "Bawan Allah kayi hak'uri zuwa gobe", Cewar Sameerah, " Nifah kud'ina kawai za'a bani", Ya fad'a cikin karaji,

    "Hayani suke bari naje naga lafiya", Lukman ya fad'a yana bud'e k'ofa, " Mai gyara ya kira babu kud'in biya",

    Bai tanka ta ba, ya fice tabi bayansa,

    Nafi'u na ganin Lukman, Ya k'ara d'aga murya a biya shi kud'in shi, Hannu yaba Nurah sukayi musabbaha, Ya tambayi nawa ne kud'in, Nafi'u yayi charaf yace "Dubu biyu", Mamaki ya hana Nurah magana, Ya zaro dubu uku ya bashi, Ya washe baki ya karb'e,

    Rahma sai yanga take, tana jin kanta sama, Dubu goma ya zaro ya mik'awa Nurah, " Ba na mayar da hannun kyauta baya bane amma nagode wanda ka biya ma ya wadatar", "Dan Allah ka karb'a, ba zan ji dad'i ba", Atafur Nurah yak'i karb'a, Yasan ciwon kansa, bashi da son abun duniya ko kad'an, muradin sa ya tsare mutuncin sa.

     Lukman bashi da wani option, dole ya mayar da kud'in ya wuce mota, " Arzik'i na kiran mutum yana guduwa, ohh Allah ya rabamu da tsiya", Cewar Rahma tabi bayan sa, Nurah sam bai ji haushi ba, ya d'auki hakan a bisa rud'in duniya dake d'ibar ta, yana mata addu'ar Allah ya taro ta.

    Sameerah sosai taji ba dad'i ba, sam bata so a wulak'anta mata Ya Nurah, Sukayi sallama ya tafi.

     Lukman ma bai jima ba, ya tafi bayan ya cika Rahma da kud'i.

   Kan katifar d'akinsu ta baje kud'in, Tana fad'in "Gwaggo zo ki gani"

    Baki ta saki tace "Kaga Dan' arzik'i ban tab'a ganin kud'i masu yawan su ba", " Yace zai turo iyayensa asa rana", Gwaggo gud'a tayi tace "Kaii wayyo dad'i mun kusa fita daga talauci", Rahma tace " Na kusa zama irin su Ameerah(K'awarta ce iyayenta nada kud'i tana gayu sosai), "Ai sai kin ma wuce su"

     "Gwaggo kinsan matsayacin saurayin Sameerah, Ya basa kud'i yak'i karb'a, ko kud'in gyaran mashin d'insa Lukman ne ya biya", " Yaron nan anyi matsiyaci, ga fad'in ran masifa shi ba kowa ba", Rahma tace "Ni ta fara tausayi dan har na hango suna fad'an kud'in cefane", Gwaggo ta kwashe da dariya, Ta jawo kud'in tana k'irgawa, " Dubu Hamsin, dank'ari munyi kud'i", Rahma tace "Rabawa za'ayi", Gwaggo ta harareta tace " Tariya zan fara miki na kayan d'aki", "Ni gaskiya a'ah, ina da lalurar yi da kud'ina", " Yar' nan ashe baki da wayo", "Shi fah zai yi kayan d'aki", Ta zuba k'arya hakane niyyarta ta tilasta mishi yayi, " Da gaske, mun huta kai kina da sa'a a rayuwa"

    Dubu ashirin taba Gwaggo, ta d'auki dubu talatin, Da k'udurin taje kasuwa gobe tayi siyayya na kece raini.

*ZEELISH*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now