4

1.3K 116 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

  *ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*K'UNGIYAR HASKE WRITER'S ASSOCIATED*💡
(Home of expert & perfect writer's).

*Tare da:-*
        *Alk'alamin*

*MARYAM IBRAHEEM*
(Ummu Hanan).

*BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

   *SATAR FITA*
         (Halayyar wasu matan).

*SHAFI NA HUD'U*

   ★★★Tashi rufaidan tayi ta d'auki husna ta kaita bedroom tayi mata shimfid'a ta kwantar da ita, sannan tazo ta xubo masa abincin har zuwa lokacin hajiyan bata daina kwantar masa da hankali ba tana k'ara tausarshi da kalamai masu dad'i dan ta fuskanci sosai d'an nata ya d'auki zafi kan abinda matar tasa tayi masa.

   Tuwon semo ne da miyar kub'ewa busasshiya dataji man shanu da zallar tsokar nama, tasashi tayi kamar wani k'aramin yaro sai dataga yaci da yawa sannan ta k'yaleshi.

    Sai wajen 9:30 na dare sannan yayi mata sallama ya tafi.

***★★★
Kamar munafuka haka tayi sallama ta shiga gidan nasu zuciyar ta cikeda tsananin fargabar had'uwa da baban ta.
   Da tsananin mamaki umman ta dake bakin rijiya tana alwalar sallahr esha'ee ta amsa mata sallamar tana binta da kallo,

   "Ke kuma lafiya kika k'ara dawowa...?"
Umman ta tambayeta tana ajiye butar hannunta.

   Kuka kawai ta fashe dashi ta wuce d'akin umman tana cigaba da kukan.

    Bin bayanta umman tayi ta shiga tambayar ta abinda yake faruwa cikin kukan tace

    "Ahmad ne yace in dawo".

    "Akan wani dalilin?" Ta sake tambayar ta.

   Kafin ta bata amsa baban su yayi sallama ya shigo, nan ya tarar da abinda ke faruwa taruwa sukayi dukansu suna tambayar ta akanme yace ta dawo gida...?" K'arya ta shirga musu tace wai saboda ya rigata komawa gida ne shine yace ta koma inda ta fito,

   "Shikenan naji naki b'angaren saura nashi, idan kuma na samu akasin yadda kika fad'a min sai ranki yayi mummunan b'aci kinsan dai halina". Daga haka ya tashi ya fita.

    Sai kuma lokacin tayi dana sanin fad'ar k'arya data sani ta fad'i gaskiya abin yafi zuwa mata da sauki akan k'aryar datayi azo a gano gaskiya kuma daga baya.

    "Kin tabbatar hakane?" Umma ta tambaya.

    D'aga kai tayi kawai.

    Kai umman ta kad'a kawai ta tashi ta shimfid'a darduma ta kabbara sallah.

Washegari kamar yadda hajiyan ta fad'a ta tura babban yayansu Ahmad d'in gidan su Rabi'an, anan babanta yakejin gaskiyar abinda ya faru tsakaninsu, sosai ranshi ya b'aci da *satar fitar* datayi dad'in dad'awa kuma ga k'aryar data sharara musu, hak'uri ya bashi sannan yace da daddare Ahmad d'in yazo ya d'auki matarshi.

    Cikin mutunci sukayi sallama da juna ya tashi shikuma ya shiga gidan.

    Tun daga yadda taga ya shigo tasha jinin jikinta aikuwa dukanta ne kawai baiyi ba a wnn ranar umma ma dataji abinda ya faru itama fad'an ta hauta dashi suka taru tamkar zasu daketa.

Kuka kawai take tana basu hak'uri tareda daukar musu alk'awarin baxata k'ara ba.

    Bayan sallahr esha'ee Ahmad yazo gidan su Rabi'an dan tafiya da ita, a k'ofar gida ya samu baban suka gaisa sosai ya bashi hak'uri tareda k'ara yimasa nasiha daga bisani ya shiga gidan dan turo masa Rabi'an.

    A cikin gidan ma umma fad'an take k'ara yimata tana k'ara nuna mata illar fita ba tareda iznin mijinta ba, daga nan tayi musu sallama ta fita.

     Ciki ciki ya amsa mata gaisuwarta, kamar mai ciwon baki, bata damuba ta hau bayan mashin d'in suka tafi.

   K'ala ba wanda ya k'ara cewa har suka isa gida.

    A tak'aice dai duk yadda taso ya kulata a ranar k'i yayi dan dole itama ta hak'ura ta rabu dashi tasan zai saukone.

★*★*★
     Washegari Rabi'a ta tashi da wani zazzafar zazzab'i da  ciwon kai ga amai da take ta faman kelayawa, dole ya fasa fitar suka tafi wani hospital dake kusa dasu.

   Gwajin farko likita ya tabbatar musu da tanada shigar ciki na tsawon makonni shidda, ai Ahmad tamkar zaiyi me dan murna dan sosai yake da bukatar Karin yara ynx husna shekararta biyar cif kuma tun daga kanta basu k'ara haihuwa ba, ba kuma planning suke ba kawai dai tsarinsu daga Allah yake.

  
    Magunguna aka rubuta mata ya siya a pharmacy'n hospital d'in suka dawo gida.

    Tuni ya manta da wani fushi dayake da ita ya shiga tarairayarta da bata kulawa ta musamman....


*Mrs Salees Mu'az*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now