3

1.2K 108 3
                                    

KUNDIN HASKE

ALK'ALUMAN MARUBUTA🤝🏻

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡💡💡

*Wattpad:-Ummishatu*

TARE DA ALK'ALAMIN

*UMMI A'ISHA*👌🏻

*BAK'ON YANAYI...!*❤
     (Kafar sadarwa)

*Babi na Ashirin da d'aya (21)*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Kada kayi alfahari saboda duniya ta aureka domin kafin ta aureka saida ta saki wani.*

*3*

     ***Kai tsaye makarantar primary ta gwamnati dake nan sabon gangare da ke cikin garin kaduna muka nufa nida haidar,babu bata lokaci muka je ofishin shugaban makarantar nan aka gama komai aka dauki haidar sai yan abubuwan da ba arasa ba wadanda za abiya da basu taka kara sun karya ba,

Gida muka dawo da zummar washe gari zai fara zuwa sannan za adinka masa uniform,baffa shine yabada dukkan abubuwan da ake bukata domin abul khair yace babu ruwansa lokacin da nayi masa maganar wannan dalilinne ma yasa ban kara bi ta kansa ba sai mu dasu innah ke yin abunmu har komai ya kammala haidar yasoma zuwa makaranta bayan ansiya masa yan littattan da ake bukata saboda koyon rubutu da karatu,

Kullum nice ke rakashi da safe har sai nakaishi naga shigarsa aji sannan nake dawowa gida haka kuma da zarar lokacin tashi yayi nake zuwa intaho dashi,shi kansa Abul khair yanzu bamu fiya haduwa ba duk da ina bukatar ganinsa,kwana biyun nan da ban ganshi ba zuciya ta har wani sauya bugunta takeyi saboda begen ganinsa,

Yau ma kamar yadda yasaba cikin dare ya sadado yazo,bayan kammaluwar komai ya karawa motarsa mai yayi gaba,dama araina inata addu'ar Allah yasa innah ko baffa basu ji zuwansa ba cikin ikon Allah kuwa da alamar basuji dinba,

Tun daga wannan ranar kuma yanayin jikina ya sauya bakina babu dadi ga hajijiya dake faman shamayata, laulayi nakeyi sosai ga shegen kwadayi tamkar mayya kullum da abinda nake so. Yau ma kamar kullum da kwadayin tsire na tashi gashi babu kudi a hannuna nikuma kunyar tambayar innah ko baffa nakeji shiyasa na yanke shawarar kiran dan zafin kan nawa akan yataimaka yasiyo min amma wayar har tayi ta katse bai dauka ba zuwa can da nasake kira matarsa ta dauka ban kai ga yin magana ba ta kare min zagi tass sannan ta katse wayar,text massage na tura masa idan yazo nasan zai gani amma shuru har dare bai biyo sakon ba,

Ina kwance lamo haidar yana jikina muka ji sallamar harun kanin abul khairi wanda kusan ma shine dan auta ahalin yanzu domin su ukune kadai suka rage awurin iyayen nasu daga Abul khair sai Rahinatu sai harun,zuwan harun yayi min dadi domin yazo da nama balangu fal takarda nan innah ta zubo min shi kaya guda nashiga daki naci nasha ruwa sai lokacin naji hankalina ya kwanta har nasamu zarafin yin bacci mai dadi.

Dawowar harun daga garin gombe inda yake karatu tabbas ya zame min alfanu acikin halin da nake ciki domin tunda yadawo shine yake dawainiya da haidar,shike rakashi makaranta idan kuma yana gida to suna tare adakinsa haka kuma nima yakan fita haka kawai yasiyo min duk wani abu wanda yasan zanso cinsa a wannan lokaci,

Lokacin da yafara bin baffa kasuwa kuwa hdima saita karu domin duk ranar da yaje to baya dawo mana hannu rabbana yakan iyo tsarabar nama da kayan marmari nikuma dama yanzu nazama kamar wata kura banida magana sai ta nama to fuskantar hakan da yayi yasashi yake yawan siyo min kusan kullum kuma kullina daban yake siyo min,hatta goro da ya fuskanci ina yawan ci shima da ankawo musu zai zabo masu kyau yataho min dasu da yake baffa dama kasuwancin goro yakeyi shekara da shekaru. Abul khair kam babu ruwansa dani musamman ma yanzu da yafi yin watsi dani fiye da da domin yanzu babu ruwansa da halin da nake ciki,harun dai shine ya zama tamkar mijina domin shine ke dawainiya dani da yarona ahaka har cikina yafito yashiga watanni biyar sai lokacinne kuma Abul khair ya farga da cikin dake jikina amma ada bai fahimta ba kasancewar rabonshi dani yau watanni uku kenan tsakaninmu sai dai daga nesa nesa,

KUNDIN HASKE💡Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt