4

42 4 0
                                    

©️Fertymerh Xarah💞

4

Yarinya taci suna AISHA amma suna kiran ta da AYUSHA, sunan mahaifiyar su Alhaji yazeed kenan wanda shine Asalin sunan Annam.Ayusha yarinya ce mai haquri tun tana jinjira bata da fitinar kuka ko hana mahaifiyarta aiki, idan kaji kukan ta tayi kashi a pampers ne tana so acire mata ko kuma tana jin yunwa.Haka rayuwa ke tafiya yau da gobe yarinyar tana girma da wayo, kusan kullum sai anyi waya da Annam she miss Ayusha yaushe Ayusha zata zo Abuja ta zauna gidan su.Halimatu kanyi murmushi a ranta tace sai bayan raina, Ayusha bazata taba zama da mahaifiya irin taki ba Annam kema ina roqo Allah yasa kada ki ɗauko ko ɗaya daga cikin halin ta domin macece marar kirki kuma bata san mutunci da darajar ɗan adam ba.Ayusha tana da shekara uku suka sanya ta nursery kasancewar bakin ta ya buɗe tana iya magana and she is active akan komai suka nuna mata, tana da gashi amma ba can sosai ba kamar mahaifiyar ta, haka fuska da muryarta duka na mata ne dalilin daya saka su cikin tsantsan farinciki na ganin cewa abinda suka zaba shine yafi rinjaye a jikin Ayusha.
Mahaifinta Alhaji yazeed dama bamai zama gari ɗaya bane business yake qasashe qasashe yake zuwa ɗauko kaya yana kawo wa nigeria ko ince sokoto ma tunda anan yake zaune da iyalinsa.Shi ɗin mai kuɗin gaske ne wanda baya bayyana hakan ga mutane, yana da taimako sosai musamman marassa shi a unguwar su kowa yana yabon sa haka baya da fitina irin ta yan kasuwa kuma baya zalunci a kasuwancin sa, shi ɗin ƙani ne ga Alhaji Abdallah wanda shima gwargwado yana da nashi kuɗin amma bai kai Alhaji yazeed ba.Su biyu ne kacal a gun iyayen su, sun mutu sanadiyar hatsarin jirgi suka barsu su biyu, sun taso tare da kakar su a wurinta suka girma sanda itama zata rasu ta basu dukiyar iyayen su, Alhaji abdallah shi ya ɗauki nauyin kansa dana ƙanin sa har suka kammala degree ɗin su na farko, anan ne Alhaji yazeed yace shi bashi da ra'ayin ci gaba da boko ya fison business wannan da yayi ya ishe sa duk inda zai je.Babu yanda Alhaji Abdallah baiyi ba akan ko masters ne ya qara fafur yaqi dalilin daya saka suka je kotu aka raba masu dukiyar su kowa aka bashi nashi, Abdallah ya cigaba da karatunsa domin yana son yayi zurfi sosai acikin ilimi yayin da yazeed ya bar qasar kai tsaye domin fara business ɗinsa.
Ganin farko da yazeed yayi wa mariya tare da Abdallah ya nunawa yayan nasa wannan matar batayi kama da matar aure ba yaya, meyasa sai ita zaka aura ga mata da yawa a gari menene a tare da ita?
Yace bazaka gane bane yazeed shi so babu ruwansa da kyau ko akasin sa, ni ina son mariya kuma tana sona meyasa bazan aure ta ba?
Yaya idan aure kake so ka auri Nadiya yar gidan mutunci, Nadiya tana son ka tun bamu kai haka ba, kasanta kasan ƙuruciyar ta kasan kalar tarbiyar ta domin ta kasance maƙociyar mu ce.
Babu son Nadiya a tare dani yazeed bayan so irin na qanwa saboda na girme ta idan na aure ta zan cutar da ita da rayuwar ta ne, idan ka matsa na aure ta bazan ƙi bin umarnin kaba saboda kana ƙanina amma nadiya bazata sami farin cikin aure ba saboda zuciyata tana tare da mariya.
Anya babu asiri a al'amarin ka da mariya kuwa yaya, wannan matar fa bana tunanin na girmeta fa?
Wannan na ɗaya daga cikin dalilin rashin jituwar mariya da yazeed tun farko wanda hakan ya shafi matarsa Halima, at times Abdallah kan zauna yayi tunanin ɗabi'u irin na matarsa rashin tarbiya da sauran su duka gaskiyar yazeed ne, gashi dai sun girma sun haifi ɗiya ɗaya amma still ta kasa hankali kuma babu wani girmansa da take gani a hakan wai auren soyayya ne suka yi.
Farkon auren su da fari yazeed a gidan yake zaune amma fafur mariya ta nuna bazata zauna da maza biyu a gida ɗaya ba tunda namiji ɗaya take aure.
Har yanzu ban fahimce ki ba Abdallah yayi maganar yana kallon ta cikin mamaki.
Ta ja ƙaramin tsaki kafin tace duk abinda nake magana akai ka fahimta kasani illah kana son maidani wata mahaukaciya ne, menene acikin abinda na faɗa da baka gane ba nace bazan zauna da maza biyu a gida ba ina auren ka wani ƙato ya tare min a masaukin baƙi akan wane dalili ni idan nawa yan uwa suka zo a ina kake so su zauna?
Yace mariya kin kuwa san ko akan waye kike wannan maganar, yazeed fa ƙanina ne wanda shi kaɗai nake dashi a duniyar nan, uwar mu ɗaya uban mu ɗaya taya kike tunanin zan iya fitar dashi daga gidannan bayan nine yayan shi kai ubama a yanzu, a ina kike so yaje ya zauna inda ya fiye masa wannan gidan?
Tace ko a rana ɗaya kuka fito babu inda addini ya yarda da hakan, ka fita office ka barni da wani ƙato a gida kai sam bazai yiwu ba yanda ƙanin nan naka baya ƙaunata wallahi zai iya kashe ni idan baka nan.
Kada ki ƙara kiransa ƙato ya faɗa tare da nuna ta da ɗan yatsansa cikin bacin rai wanda hakan ba ƙaramin sosa mata zuciya yayi ba sai ta fashe da kuka mai tsanani tana soma haɗa kayanta alamar zata bar gidan nan kuma hankalinsa ya tashi ya soma magiya da bata haquri amma sam taƙi sauraren sa.
Sun fito falo daga bedroom suka sami yazeed xaune akan sofa da gwangwanin malt a hannunsa yana sha yana danna wayarsa.
Cak suka tsaya duka su biyu suna kallonsa, jin motsin su ya saka shi ɗagowa yana kallon su kallo ɗaya yayi  mata ya ɗauke kansa xuwa ga yayan sa yana yatsina fuska kamar yaga kashi,
Yaya lafiya kuwa?
Yace ba komai is our personal issue, yazeed ya tabe baki tare da ɗaga kafaɗarsa yana cigaba da latsa wayar sa, kalaman Abdallah na ba komai suka qara tunzura ta cikin bacin rai take kallon sa,
Tace kace ba komai fa,
Yace eh nace ba komai wannan tsakanin mu ne ki shigo daga ciki mu ƙarasa maganar.
Wallahi idan har kaga na dawo gidan nan har na shiga wannan ɗakin tabbas Yazeed ya bar gidan nan..., ta faɗa cikin ɗaga murya da bacin rai tana nuna sa da yatsa.
Da sauri yazeed ya ɗago yana kallon ta jin furucin ta kafin ya dubi yayan nasa yana jiran nasa hukunci, zai zabi matarsa ne yabi umarnin ta ko ya, ga mamakin sa yaji yayan sa na faɗin.
Yazeed ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya bazan gaji da gayamaki hakan ba, bani da wani ɗan uwa kamar shi kuma shi ɗin amanar iyayen mune, bazan zabe ki akan sa ba, kije kawai Allah ya sada mu da alkhairi idan akwai rabo tsakanin mu.
Ta fashe da kuka mai tsanani cikin takaici da bacin rai, ka zabi ɗan uwan ka sama dani wallahi ka cuce ni, na tsani kaina a yau for trusting you, ashe haka kake mayaudari, ashe baka sona duk soyayyar da nake nuna maka.
Ki min shiru maƙaryaciya, kina sona ne bazaki so jinina ba, ki gayamin menene laifin yazeed why did you hate him?
Tace saboda shima baya sona....
Yazeed ya katse ta, is ok malama mariya i cant respect you by calling you anti or any other name since you dont have respect for my brother, a kullum zan gayamaki ke ba mace mai tarbiya bace, ba kisan menene aure da haqqin sa ba, zan bar gidannan kamar yanda kika buƙata but not for you, for my brother bana son sunan sa ya baci a waje daga auren sa ya soma rabuwa da matar sa, bana so na zama mutum mai son kansa da yawa fiye dana ɗan uwansa....
Babu inda zaka je yazeed, Abdallah ya katse sa,
Dole zan tafi ya faɗa yana maida wayarsa aljihunsa, idan na cigaba da zama da wannan matar a wannan gidan zumuncin mu zai yanke saboda zan iya mata rashin mutunci, bani bane bata son gani a gidannan zan barsa dama garin Abuja zan koma da zama a sokoto inda yan uwan mu yaya kayi haquri nasan ba laifin ka bane.
Ajiyar zuciya mariya ta saki tare da faɗin Alhamdulillah ta sami guri ta zauna tana goge hawayen fuskarta cikin murmushi alamar farin ciki, duk suka zuba mata idanu suna kallonta cikin mamaki.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now