Shafi na biyar

1.8K 163 11
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Haske Writer's Association*💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*RAYUWAR WASU MA'AURATA...*

*NA*

*UMMU BASHEER*



*Babi na goma sha uku*


Page 6

Layla ba karamin hakuri take yi ba. Domin kam yanzu abin yayi yawa gana uwar miji ga na kishiya. Dan yanda Mami ke ji da Hameeda sai hakan ya bata daman yin abinda take so a gidan. Hatta Rayyan ko wani abu yayi mata sai ta fad'a ma mami haka ko zaiyi ta shan fad'a.

Wata kusan hud'u kenan yanzu da yin auren nasu Amma Mami shiru bata ga alamar Hameeda nada ciki ba. Duk ta sake damuwa Dan ita tana son ganin jikan ta.

Layla ce kwance kan kujera ta daura kan ta kan cinyar shi. Yana shafa gashin kan ta.

"My wifey naga duk kin canza ne, ko dai na baki a jiya ta ne"

Cikin dariyar maganar shi tace"kai Dear how can this be possible? "

"Kina mamaki ne da ikon Allah ?"

"A'a My love ina dai tunani ne"

"Tashi ki shirya muje hospital na gwada ki"

Ba tare da tayi mai musu ba ta shirya suka nufa hospital.

Suna zuwa ya fara Mata tests ai ko gwajin farko ya nuna tana dauke da ciki.

Gaba dayan su ba karamin farin ciki suka shiga ba.

Suna ta ma Allah godiya sosai.

Koda suka koma gida sai basu fad'a ba.

Sannu a hankali sukayi ta rainon cikin har ya shiga wata hud'u.

Rayyan ba karamin hakuri yake da Hameeda ba. Domin ta cika shegen yawo. Ga rashin kunya dan ko Mami bata kyale ba . Yanzu har fad'a suke da Hanan sai take ganin ashe gara Layla da Hameeda. Nan Hanan ta fara nadamar abubuwan da take ma Layla din. Mussaman taje ta bata hakuri.

Layla taji dad'in hakan domin ko ba komai yanzu suna shiri. Tana fatan Allah ya daidaita tsakanin ta da Mami.

***************

Milhan iya hakuri Yana yi Amma abin na bakan ta mai rai.

Wata rana ya shigo Dakin Ramla Yana neman wasu takardun shi kawai sai yaci karo da wasu magunguna Yana dubawa sai yaga maganin family planning ne. Hankalin shi ya tashi. Bai tab'a tunanin Ramla na shan maganin Hana daukar ciki .

A parlour ya same ta da maganar nan ta shiga wayancewa. Fad'a sosai yayi Mata yace mudin tana son cigaba da Zama dashi ya zama dole ta daina shan magungunan nan. Domin shi har ga Allah Yana son haihuwa.

Da daddare yaje gidan su nan ya tarar da sunyi baki. Kanwar Maman shi ce da yaran ta su biyu .

Suna tare da kannen shi duk suka gaishe shi.

Kallon dayan yayi. Sai yaji gaban shi ya fad'i.

A haka yayi ta tunani a ranshi har ya tafi gida.

Kwana biyu Amma hankalin shi ya kasa kwanciya domin kam ya fad'a tarkon son Yar 'uwan shi.

Koda yaje gidan su sai yaga ashe suna nan . Haka ya yini kawai Dan ya dinga ganin ta.

Juwairiyya budurwa ce nutsatsiya ga ladabi. Tana da shiru shiru babu ruwan ta. Yanzu ta gama secondary school dinta.

Sosai Milhan yake son Juwairiyya Dan Koda suka koma Garin su sai da yaje. Ya sanar mata da abinda ke zuciyar shi. Kuma ta amince da shi.

Soyaya sosai sukeyi tsakanin su Dan har manya sun shiga maganar ansa ranar aure wata biyu.

Ramla ko kad'an bata sani ba.

Sanu a Hankali har lokaci yayi domin saura sati biyu.

Milhan yayi gyaran gidan sosai ita dai Ramla sai mamaki take.

Ana saura sati daya auren nasu Milhan ya sanar da ita.

Ai ko ba karamin hauka tayi ba sam ita bata yarda da kishiya ba. Shi dai ya bata hakuri taki hakura Dan haka ya kyale ta.

Babu irin haukar da bata yi ba amma Allah ya Kaddara sai anyi auren domin satin na zagayowa aka daura auren Milhan da Juwairiyya.

Aka kawo ta gidan ta. Ramla fa kishi kamar zata mutu sai yan uwan ta dake bata hakuri.

Kwanan Juwairiyya biyu ta fara fuskantar matsala daga gurin Ramla.

Milhan duk baya sani. Zuwa take ta zage ta tass tace auren na munafunci ne.

A haka akayi wata biyu. Sam Juwairiyya bata Jin dad'in Zama da Ramla Dan ba karamin wahala take sha ba.

Gashi cikin ikon Allah ta samu ciki. Ganin hakan ya kara tayar da hankalin Ramla.

Milhan ko ba karamin farin ciki yake ba. Yanzu ne yasan yayi aure. Dan ko duk abinda ya rasa ada yanzu Yana samu.

Matsalar shi dai Ramla Dan duk lokacin da ita keda girki Yana shan bacin rai.

*******************

Baiwar Allah Husnah tana ta fama da laulayi. Ga auyukan Safwan. Yace tayi mai wannan yace tayi wannan. Bata tab'a nuna mai gajiyan ta ba. Shi bai ma lura da bata Jin dad'i ba domin bata gaban shi.

Tun daga bedroom yake Kiran ta Amma tana kitchen bata ji ba.

Kitchen din ya shigo a fusace Yana zuwa ya dauke ta da wani Mari. Ba karamin azaba taji ba nan ta dukuna ai sai ya fara'a ball da ita da gudu ta nufa parlour nan ma ya bita Yana zuwa ya hada kanta da bango.

Ihu ta saki ta fad'i a kasa.

Hannun shi yasa ya damko gashin ta da karfi.

Tsawa ya daka Mata "Dan uban ki ni Zaki yaudara?, ashe ban fad'a miki mudin kina son Zaman gidan nan ba to babu haihuwa? "

Kuka take yi "Kayi hakuri Dan Allah "

"Shut up you stupid, wato har hospital kike zuwa ko ai naga takardun naga komai. Bana bukatar cikin "

"Kayi hakuri Allah ka kyale ni wallahi zan mutu cikina ciwo "

Buge bakin ta yayi Ranshi a bace. Ya Kai ma cikin duka ihu ta saki. Ya dauki kafa sai hamb'ari cikin sai Jin sallati yayi. Cak ya tsaya.

Juyowar da zaiyi sai ganin Mommy yayi a tsaye.

A rude tace"Safwan kashe musu Y'a za kayi ?"

Da sauri yaja baya. Ganin ta rufe ido ga jini na zuba sosai a kasa yasa mommy yin kanta da gudu tana ture Safwan.

Driver ta Kira ganin halin da Husnah ke ciki. Nan da nan suka nufa hospital da ita. Suna zuwa aka karbe ta.

Bayan Dan wani lokaci aka fito da ita zuwa Dakin hutu. Nan suka sanar ma da Mommy tayi Barin ciki. Kuma sannan bata cin abinci ga damuwa yayi Mata yawa. Hankalin ta a tashe ta Kira Baban Safwan ta sanar mai halin da ake ciki shima ranshi ya b'aci sosai. Nan yazo hospital din.

Tun Bayan tafiyar Mommy da Husnah hospital. Wata tsoro da nadama suka saukar ma Safwan. Sai yaji kunyar bin su hospital din har zuwa dare sannan ya Kira driver mommy ya tambaye shi inda suke.

Koda yaje tun kafin ya shiga Dakin mommy tace. Kar ya kuskura ya shigo.

Lalai ba karamin abu yayi ma mommy ba tunda tayi mai haka .

Bayan kwana biyu aka sallame su daga hospital. Mommy direct ta wuce da Husnah gidan ta. Domin tace ba zata koma gidan Safwan ba. Tunda neman kashe ta yake. Gashi ya zubar Mata da ciki.

Husnah kwanan ta biyu gidan Mommy tana Jin dad'in Zama sosai Anan. Sannan mommy bata Barin ta tayi aikin komai. Barci take samu sosai. Sannan mommy tana yawan sata cin abinci.

Yanzu tana cikin kwanciyar hankali.

Masu karatu ku cigaba da Bina domin Jin karshen labarin nan.

*UMMU BASHEER CE*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now