Shafi na biyar

1.3K 106 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*

  *shafi na biyar*

Juyawa sadiya tayi abinta tabarsu nan shaye da mamaki shukra ce cikin fushi ta soma magana "gaskiya iskancin anty sadiya ya fara yawa mama dubi kasusuwan kaza da uban kabiji da ta kawo mana,saikace wasu kuraye ko akuyoyi ne mu da zata kawo mana uban kabeji?mama bani ledar kazar nan dan allah inkaiwa yayanmu yaga abinda matarsa tayi"

Murmushi mama kawai tayi ta jinjina kai sanan tace "shukra kada wanan ya dameku kada ku manta itama fa mace ce zaayi mata ko baayi mataba zaayiwa mamanta wanda yafi wanan kuma na tabbata zaiyi mata ciwo,nidai nasan da zuciya daya nake zaune da ita kuma kallon yar dana haifa a cikina nakeyi mata dik abinda ta shuka shi zata girba shukra,maganar kaiwa abubakar ma bai tasoba wallahi dan bazan zama silar hadasu rigimaba muyi hakuri muci wanan din"

  "gaskiya mama hakurinki yayi yawa wace suruka ce ta ke kyale matan danta?ina taga fuska ma balle tayi mata iskanci?to wallahi mama ni zanfara daukar mataki don abubuwan sadiya sunfara wuce gona da iri"

  "babu matakin da zaki dauka insha allahu nan gaba zata gyara,idan bata gyaraba duniya zata gyarata kuyi hakuri kusa mata ido"

"A haka ne yaya ke cewa mufara hada girki da ita?tabdijan to wallahi mama kada ma mufara dan wanan shegiyar matar watarana da yunwa zata barmu"

Ajiyar zuciya mama tayi tace "dik ya wuce shukra hada girki kuma a barta tayi mugani kinga abubakar ya rokeni alfarma idan naki yarda zaiga kamar wani abu ne"

Shukra bakin ciki ya hanata kara cewa komi sai jefi jefi da take sakin kwafa....

******
A dakin sadiya kuwa abubakar bayan ya fito wanka ya zauna ya cinye abincim da sadiya tayi tass yanaci yana santi,tsintar kansa yayi cikin nishadi yau din nan da ya kara tabbatarwa da kansa sadiya ta shiryu ta daina kishi da mahaifiyarsa,

Bayan ya gama cin abincin ne sadiya tanata tunanin yadda zatayi tsarki da abinda bintu ta kawo mata batare da ya gani ba dabara ce ta fado mata take ta kakalo murmushi a fuskarta tace "sweet kaje dakin mama hira mana nima bari inyi wanka in shigo ayi hirar dani"

Wani dadi ne ya lullube abubakar da yaji abinda sadiya tace batare da yace komiba fuskarsa dauke da murmushi ya manna mata light kiss a lebenta sanan ya juya ya fita,
Yana fita ta daka uban tsalle cike da murna da farin cikin burinta ya kusa cika ta fada bedroom dinta ta cire kaya ta shiga bayi don yin wanka....

Mama na hango tahowarsa ta jikin labule ta kauda ledar kasusuwan da sadiya ta kawo dan bazataso ya gani suyi fitina ba da sallamarsa ya shigo fuskar sa dauke da faraa yadan tsugunna cikin ladabi "barka da hutawa mama"

Itama murmushin tayi mama ta amsa mishi "barkadai abubakar har an fito?"

     "eh"

"dama nakosa ka shigo saboda wata muhimmiyar magana da nakeso mu tattauna nida kai game da jalin da kabani nace mai zai hana tunda ankusa fara azumi na siyo injin nika muci kasuwar azumi dashi tunda kaga unguwar nan babu wata sanaa da zanyi wadda babu wanda keyin irinta kaga kuwa injin markade yayi karanci kuma na ruwa zan siyo yadda koba wuta zamuyi nika lafiya lau"

"mama ai dik abinda kika yanke daidaine mama allah ya bada saa yasa ayi kasuwa,yanzun zuwa jibi sai a siyo injin din ko?"

"ehh abubakar jibin yayi allah yayi albarka"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now