16

1.8K 210 23
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


16


Bata kuma kallon inda kayan suke ba tayi wucewarta daki ta kwanta, tayi iya kokarin ganin ta kauda damuwar ranta lkci daya kuma bacci ya dauketa. Cikin bacci taji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Nafisa xaune gefenta, mikewa xaune tayi, Nafisa tace "Ke akwatuna nake gani a waje, na waye?" Fatima ta d'an yi murmushin karfin hali tace "Nima yanda kika gansu haka na gansu Nafiee" Da mugun mamaki Nafisa tace "Toh wa ya kawo su?" A takaice Fatima tace "Elbasheer" Nafisa ta dafe kai tace "Lallai gayen nan really mean it, what did u think will be his main purpose of wanting to marry you Fatima? Wllh am just afraid no one knw his intention fa, yanxu haka xa ki yi shiru kiyi ta boye gaskiya a maku aure da wannan mutumin?" A hankali Fatima tace "I don't knw his intentions, and I don't want to knw, ni dai abinda na sani shine in dai ya kuskura yyi making mistake din aurena I will make life miserable for him the way he is making mine right now, ni yanxu na daina sa ma kaina damuwa in sha Allah, I am just waiting in ga iya gudun ruwansa" Nafisa tace "Ikon Allah, to me Ammi ta ce da ta ga akwatunan?" Fatima ta girgixa kai tace "Ni tun daxu da na dawo daki na shigo nayi kwanciyata kawai, na gaji da kuka Nafisa, did I deserve all this?" tana magana ne hawaye cike manyan idonta, Nafisa ta lumshe ido da damuwa tace "Kukan ba shi ne mafita ba Amira" Shiru fatima tayi a ranta tana tunanin farkon ranan da Husnah ta tilastata ta yi following din Elbasheer, Muryar Nafisa taji tana cewa "Har yanxu kuma bbu labarin Husnah koh? I saw her mum yanxu da na shigo tare da su Ammi" wani murmushin takaici Fatima tayi tana kallon Nafisa tace "Trust me Nafisah, I promise Husnah will surely pay for all I passed through, ban kyaleta ba, ita ma xata ji in da dadi ko babu" share hawayen dake sakko mata ta shiga yi wasu na kuma sakkowa, Cikin sanyin murya Nafisa tace "Noo, don't cry anymore Besty, kinsan abinda nake tunani..... Wllh sai nake ga kamar Elbasheer shine mafi alkhairi a gare ki shi yasa duk hakan ke faruwa... Kinga kuwa in har haka ne kam a sanadin k'awa kin ga jarabawa sannan kuma kin hadu da abokin rayuwar ki...." Katse ta Fatima ta yi cikin rawar murya tace "Idan kuma ba haka bane ba fah?" Nafisa ta sauke ajiyar xuciya tace "Hakan ne ma in sha Allah, beside ina tunanin kamar son ki mutumin yake tsakani da Allah banda haka taya xai yi ta bibiyar macen da ya ri ga da ya ka keta mata hadi?" Hakan da Nafisa ta fadi yasa fatima ta rushe da kuka sosai tace "Toh ni cewa nayi ina son sa Nafiee" Nafisa tace "Noo, da baki son sa tun farko baxa ki je gidansa ba duk da xugin Husnah, may be da can you have soft spot for him a xuciyar ki" Fatima ta girgixa kai muryarta na rawa tace "Nooo" Nafisa ta kamo hannunta tace "That's just it Friend, wannan mutumin ya riga da ya san ki a mace kuma yake ta bin ki yana son auren ki, sannan ki tuna fatima idan har ba shi din ya aure ki ba da wani idon xa ki kalli mijin da xai aure ki bayan ya gano ke ba budurwa bace, a kaddara Umar ne, me xa ki ce masa, me kuma xai dauke ki tunda bbu Wanda kika fadi ma gaskiyar abinda ya shiga tsakaninku da mutumin" Fatima ta hade kai da katifa tana kuka a hankli, Nafisa tace "Kiyi hakuri ki bar ma Allah komai, bayan wannan kuma ni ban san me xan ce maki ba kawata" Fatima ta dago kanta tace "Toh me xan ce ma Umar" Nafisa ta yi shiru bata ce komai ba, Mikewa Fatima tayi ta dauko wayar ta ta mika ma Nafisar tace "Ki duba text din da yyi min ban duba ba har yanxu" Nafisa ta amshi wayar ta shiga messages ta bude, dai dai nan kira ya shigo wayar, Nafisa tace "Lah ga shi ma ya na kira" Karban wayar Fatima tayi ta na kallon screen din gabanta na faduwa, can ta daga ta kai kunne bata ce komai ba, Sallama yyi ta amsa a hankali sannan ta gaishesa, yace "Lafiya lau Amira, ya gidan da su Ammi" ta sauke idonta kasa tace "Lafiya lau" yace "Hope baki yi fushi ba I didn't call all this while, I even sent you a text msg jiya da daddare ban san ko kin gani ba" shiru ta d'an yi kafin ta girgixa kai tace "Ban gani ba" yace "Ohk, ban ji dadi bane kwana biyu, I was even hospitalized but Alhmdllh yanxu" tace "Ayya ban sani ba, Allah ya sauwake" yace "Ameen, shi yasa na maki
message but baki gani ba" tace "Uhn, Allah ya sauwake" yace "Amin nagode" shiru ta yi, yace "Toh shkkn dear anjima xan shigo ki gayar min da su Ammi" ta kalli Nafisa kafin tace "Allah ya kai mu" sallama yyi mata ya katse wayar, bude text din tayi taga sanar mata kawai yyi ba shi da lafiya yana asibiti, Nafisa tace "Ikon Allah, toh yanxu ya xa kiyi da Umar Fatima?" Fatima bata ce komai ba na kusan minti daya, lkci daya wasu sabbin hawaye ya cika idonta a hankali tace "Nafisa I will tell him everything idan ya xo anjima" Nafisa tayi tagumi, Fatima na goge idonta cikin sanyin murya tace "Ai da na ji maganan Ammi tun lkcn da take kkrin rabani da Husnah da duk hakan bai faru da ni ba, da naji maganan ki nacewa in raba kaina da Husnah da...." Kasa ci gaba tayi Nafisa ta rungumeta tace "Irin taki kaddarar kenan Amira, so just accept it.... All is well in sha Allah" Sai kusan magrib Nafisa ta wuce bayan ta tabbatar ta kwantar ma kawarta da hankali ta kuma fadi mata abinda ya kamata ta fadi ma Umar idan ya xo anjima. Fatima na idar da sllhr magrib ta shiga dakin Ammi don xuwa lkcn bbu kowa gidan, xaunawa tayi duk jikinta a sanyaye, Ammi dake kan darduma cikin sanyin murya tace "Fatima yanxu kawunnan ki sun kyauta kenan, an taba aure haka kamar a film, yanxu ya suke son ayi da Umar, Umar ya cancanci haka? ban san da idon da xan kallesa ba, kawunnan ki basu taba min komai ba amma wannan karan sun min, ina tunanin da mahaifinku na raye baxai taba bada 'yar kai tsaye haka ba" Fatima ta hade kanta da gwiwa xuciyarta na kuna kukan ma ta kasa, duk tausayin mahaifiyar tata ya cikata, tasan ita ta ja mata wannan bakin cikin da take ciki..... Ammi da ke share hawayen idonta tace "Yanxu me yan anguwa xa su dauke mu, masu kwadayi da son abun duniya da kai kai inda Allah bai kai mu ba, banda haka sayar da ke nace xan yi da xa a kawo maki akwatuna har goma, amma komai ya faru ke kika jawo mana, kika yarda kika biye ma k'awa mara tarbiyya, me kwadayi da dogon buri mara godiyar Allah, da yake ke din ma makwadaiciya ce da dogon burin kika biye mata kika ja ma kanki abun kunya kika kai ma namiji kanki da mutuncin ki har gida Fatima, me na rage ki da shi, duk kokarin da nake maki bakya gani sai da kika watsa min k'asa a ido...." Fatima ta hade hannayenta tana shessheka tace "Don Allah ki yafe min Ammi, kiyi hakuri ki gafarceni" Ammi dake kuka tace "Babu wani yafiya da za ki ce in maki" kasa cewa komai Fatima ta yi banda kuka, taji duniyar tayi mata xafi, da ma ta gode Allah a yanda ya bar su bata yi hange hange ba, da kyar tayi karfin halin tashi ta koma dakinsu tana jin mugun tsanar Elbasheer, kiran Umar ta gani har uku a wayarta, don a dai dai lkcn ya katse, sake bugowa yyi ta dauka nan ya sanar mata da yana waje, ta fita ta wanke fuska sannan ta dawo ta sa hijab ko Ammi bata gaya ma ba ta fita. Kanta a kasa ta isa gun dakalin da yake xaune ta xauna, murya can kasa ta gaishesa ya amsa yana kallon ta yace "Are you okay Fatima" ta gyada masa kai tace "Yeah" duk abun nan bata yarda sun hada ido ba, tace "Ya jikin?" Yace "Alhmdllh naji sauki, ya su Ammi?" Tace "Suna lafiya lau" da damuwa yace "but you look depress tell me what's wrong dear, ki gaya min don Allah" tayi iya kkrin ganin bata fara kukan dake cin ta ba, tace "Ina son muyi magana da kai pls" kallon ta kawai ya tsaya yi kafin yace "Toh ina jin ki" sai da ta gama gathering din courage dinta gaba daya cikin sarkewar murya tace "Umar kayi hakuri... you knw God plans best, may be we where neva destined to be together...." Mikewa yyi da sauri yana kallon ta, ta ki yarda ta kallesa, a hankali yace "Ban gane ba Amira, what did u mean" ta hadiye abu da ya tsaya mata tace "So nake ka hakura dani don Allah don annabi, don darajar mahaifanka, Allah kuma xai baka warce ta fi ni" muryarta na rawa ta kare, kallonta kawai yake ko kiftawa bbu, ta hade hannayenta tace "For Allah's sake kada kace min A'a kuma kada ka tambayeni me yasa, just tell me so be it" Sosai idonsa ya kada, ya kauda kai na kusan minti biyu, tana sheshsheka tace "Kayi shiru Umar, talk to me plss, ka min abinda nake so, Allah xai mayar maka da mafi alkhairina, for Allah's sake ka min abinda nake so idan har son gaskiya kke min" Juyowa yyi yana gyada kai cikin cracky voice yace "Shkkn Fatima, Allah ya sa hakan shine mafi alkahiri, Allah hada kowa da rabonsa, amma ina fatan xan iya ci gaba da xumunci da su Ammi koh?" yana kai wa nan ya sa hannu ya share hawayen da ya taru idonsa, ta girgixa masa kai hawaye na sakko mata tace "Har ni ma ba da su Ammi kadai ba" kai kawai ya iya gyada mata, cike da karfin hali ta durkusa kasa tace "Nagode Umar, amma ka yafe ni don Allah kar ka bar ni a xuciyar ka" kai ya gyada mata nan ma da karfin hali yace "Na yafe maki" tashi tayi ba tare da ta sake kallonsa ba tace "Nagode sai da safe" daga haka ta wuce ciki da sauri, fadawa kan katifa tayi ta dinga kuka kamar an aikota, tun daga ranan da ta jona rayuwarta da Elbasheer take kuka ita da a da sai tayi watanni bata yi hawaye ba, har dare ya raba ta kasa bacci, tana son tashi ta dauro alwala tayi sallah amma duk jikinta yyi mata nauyi, haske wayar ta yyi ta jawo a hankali tana kallon screen din, message din Umar ne ya shigo, jikinta yyi mugun sanyi ta tashi xaune a sanyaye ta bude message din, "A duk xaman mu Fatima idan har na taba saba maki cikin rashin sani ko akasin haka kiyi ma Allah ki yafe min, nima kuma na yafe maki duk da baki taba min komai ba, ina maki fatan alkhairi a rayuwa, Allah kuma ya albarkaci rayuwar da xa ku yi da El-Basheer in sha Allah, I am wishing you nothing but all goodies that life gat for u Amira, in sha Allah xan koma kano gobe, ban ji dadin baxan ma Ammi sallama ba xan wuce amma idan da rai we shall meet once again in life, I never regret knowing you teemah" content din message din knn, ta tura wayar ta ja bargo ta rufe har kanta.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now