Shafi na 6

4.4K 285 5
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al K'ALUMAN Marubatan HASKE_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
           *NANA DISO*

*DARAJAR MUTUNCIN MU.....*
       _('yan zamani)_

     
BABI NA DAYA
    Shafi Na SHIDa...

Tunda Allah yasa aka saka ranar bikin walida da fatima dukkanin gari ya dauka ga arzukin da mahaifin su yayi kowa sai cewa yakeyi tabbas shi arzuki lokacine indai kanada rabo to zaka samu...

   Yau jummaa walida tana zaune ta fashe da kuka cike da radadi acikin ranta..

   "Hajjaju ce tace wai wani irin kuka kikeyi walida me isa kikewa kanki haka kinaso ki illata kanki ne Allah ai gafurrur rahim ne..

   " wallahi hajiya bazan iya daina kuka da farin ciki ba ni dana kasance ina aikata zunubai nayi sabo kala kala amma ki duba niimar da Allah yayi min har yabani miji nagari mai sona saboda Allah tayaya bazanyi kuka ba nakara jin tsoron Allah.. wallahi ban cancanci haka ba hajiya takara saka kuka...

   " haba walida ai tsakanin bawa da Allah baa shiga indai har kanemi yafiya zai yafemaka kuma karki manta jarabawa ce tunda Allah haryasa kika gane hanyar daidai ai sai kiyi hakuri kidaina kuka...

   " Toh hajiya inshaaAllahu Allah ya yafemun yakuma tsaremu daga mummunar kaddara..

   Gida yayi kyau yan'uwa sai zuwa Allah sanya alheri sukeyi.

  Muazzam yana zuwa aka kaishi setroom walida ta fesa turare tazo zata tafi wata aunty dinta tace gaskiya yayi kokari da ya kwashi karuwa...

    " walida da kwallah ta cika mata ido tace zaki iya hana yin Allah ne? Ko kuma zaki iya goge kaddarar Allah? Kun dauki karan tsana kin doramin haka kurin sai kace nataba yimiki wani abun sannan tasa kuka...

   " Dallah malama tsaya sai da kikagama karuwancin naki shine zakizo ki nuna ke ga gari ce banza kawai...

  " muazzam ne yafito daga setroom yaga aunty yabi sai ciwa walida mutunci take ita kuma takasa magana sai kuka takeyi..

   " haba anty yabi wannan kalaman naki ai basu dace dake ba yar yayarki ce fa yaza'ayi kina fadar irin wannan...

   " kai muazzam in banda taje ta asirce ka ta mallake ka tabada mutuncin ta anyi mata aike ai har wannan abar aura ce ga yaranmu kyawawa kuma yan gayu masu addini su suka fi dacewa dakai...

    " Muazzam ne yayi dariya yace walida banson kukannan kinji dake zan zauna har abada kuma soyayyarki taba raina har abada bazantaba daina sonki ba kuma kaunarki kullum ginuwa takeyi ke kuma anty yabi wallahi wallahi baki isa kirabamu ba wannan tsokar cikina ce babu wanda zai raba sai allah koma me taje tayi ko karuwancin ne ina son abata ina kuma kaunarta kuma itace uwar yarana walida kece farin cikina kuma abokiyar rayuwata...

   " ohoo maka kai kasani kar dai aje akwashi kanjamau..

   " muaazam yace tohh sai me in nakwasa ai ni nakwasa ba ke ba sai ki gode Allah...

   Ke kuma walida kada kikara kuka akan abubuwan da suke fada kinji Allah ke tsara komai ba bawa ba...

   " Tabbas yau nakara tabbatarwa DARAJAR MUTUNCIN MU KUDI BAYA SIYA.. talauci ko arzuki sai abunda Allah yatsara mana yaaAllah kayafemin nayi abu bisa son raina kuma muazzam karka manta fa bazan iya goge tabon danayiwa kaina ba..

   " Walida kenan wanene yake ja da ikon Allah bayan komai mukaddari ne matata uwar yarana fitilar zuciyata muazzam naki ne har abada kinji kuma sai na zamar miki abun Alfahari nidai abu daya nakeso kiyi shine hakuri a cikin zaman mu kinji sahibata..

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now