BABI NA 18-UMMU HANAN

1.6K 133 6
                                    

*KUNDIN HASKE*

   *ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*K'UNGIYAR HASKE WRITER'S ASSOCIATED*
(Home of expert & perfect writer's).

*Tareda da:-*
     *Alk'alamin*

*MARYAM IBRAHEEM*
(Ummu Hanan)

     *BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

*SHAFI NA D'AYA*

   *SATAR FITA*
        (Halayyar wasu matan)

   *Bismillahir rahmanir raheem*

Madaidaicin gidane mai dauke da d'akuna biyu da kitchen da band'aki, an gyara ko Ina tsaf daga gani dai mamallakin gidan yana cikin rufin asiri.

Matashine d'an kimanin shekaru 30 ya fito daga d'aya daga cikin d'akunan cikin shirinshi na fita yayin da wata mata ke biye dashi a bayanshi da alamu dai itace matar gidan.

    "To ni zan fita".
Ya fad'a yana gyara zaman hularshi.

   "To Allah ya kiyaye....amma....shiru tayi bata k'arasa abinda tayi niyyar fada ba.

  "Wani abu ne...?
Ya tambayeta idanunshi a kanta.

    "Dama mgnr zuwa gidan bikin nanne na tambayeka banji kace komiba" ta k'arasa mgnr cikin inda inda.

   Tsayuwarshi ya gyara yana mata wani irin kallo, baki ta turo tareda juyar da kanta gefe.

   "Wai meyake damunki ne Rabi'a?...uhm? Tun jiya ai na fad'a miki ba inda zakije, idan ke bakya kishin kanki toni Ina kishinki kwana nawa kika jera kina fita? To ba inda zakije".

   Fuska ta b'ata tace
"Haba Abban husna kasan fa yadda muke da bushra amma ace ta gayyaceni bikin k'anwar ta banje ba saboda Allah..?

   "Na fad'a miki dai wllhi" daga haka yasa kai ya fita.


   Juyawa tayi ta shige d'aki tana faman mita
   "Aiko wllhi kamar da k'asa sai naje idan mutum bayayi taya shima za'ayi masa idan hidimarshi ta tashi.

    Nan da nan tayi wanka ta shirya cikin sabuwar atamfarta ankon sunan mak'ociyarta zainab, fitowa tayi ta kulle gidan ta shiga gidan zainab d'in dake jikin nata gidan.

   Zaune ta sameta a d'aki tana shayar da jaririyar y'arta data haifa.

   "Maigidan ya fita ko..? Ta fad'a tana shiga cikin d'akin.

   Murmushi zainab tayi tace
   "Kema dai Rabi'a sai kace baki saniba ai kinsan baban waleed tun sassafe yake fita, ki zauna mana".

   A'a ba zama nazo yiba sauri nake fad'a miki nazo yi husna xata shigo nan idan an tasosu daga makaranta na fad'a mata".

   Harararta zainab d'in tayi tace
  "Ke kiji Rabi'a da wata mgn sai kace yau aka fara, yau kuma Ina za'a k'afar yawo..?

   "Bikin k'anwar Bushra mana kedai nasan ba zuwa zakiyi ba kina jego, Abban husna ma fa bai saniba".

   Kai zainab ta shiga girgizawa cikeda takaicin mak'ociyar tata tace

   "Yanzu saboda Allah Rabi'a bazaki daina wannan halayyar taki ba ta *satar fita?* Har yaushe hankalinki zai kwanta ki fita ba tareda iznin mijinki ba?...kinga ni ba surutu nace kimin ba kinga tafiya ta gara inje da wuri dan in dawo da wuri yanzu mutane sai kanayi sannan kaima zaayi maka". Daga haka tasa kai ta fice daga gidan cikin sauri.

   "Allah ya shiryaki ya ganar dake". Zainab d'in ta fad'a tana mik'ewa ta kwantar da d'iyar tata kan kujera ta fito tsakar gidan ta fara gyarawa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now