5

135 9 1
                                    

©️Fertymerh Xarah💞

*AYUSHA*

5

Amma ke.....Yazeed yayi saurin katse sa,

'Bar ta yaya kada kace komai, kayi haƙuri da decision ɗina ka zauna da matar ka lafiya domin auren shine daraja, da sauri ya juya ya bar falon Abdallah ya bi bayansa.

Shewa ta saki cikin farin ciki tana binsu da harara tafi nono fari haka kawai kazo ka tare min a gidan duk abinda nake idon ka akaina, ina ma mijina kwalliya kana kallewa musamman dan kawai kaga Allah yayi min halitta ta mazaunai, kwalelenka domin sun fi ƙarfin ka wlhy shashasha kawai.

Wannan dalilin ya saka shi barin Abuja ya dawo sokoto da zama, ko bayan auren sa da Halima bai taba xuwa da ita gidan yayan nasa ba shima bai qara xuwa gidan nasa ba, duk yaje Abuja a hotel yake zama daga baya ne ya yanke shawarar siyen gida saboda yana da iyali bai kamata yana yawon zuwa hotel da ita ba.

Halima mace ce mai kirki da tarbiya gwargwado tana masa biyayya kuma tana son sa tare da kaucewa duk wani abu da zai bata masa, ɗan adam ajizi ne dole akwai watarana da zaka kauce amma kaso tamani daga cikin ɗari duka biyayya ne a auren ta, ta taso gidan tarbiya da mutunci kuma itama ɗin gidan su suna da rufin asiri su ba masu kuɗi ba kuma ba talakawa ba, nutsuwa da hankalinta ya saka yazeed auren ta kuma har xuwa yanzu da suka haifi Ayusha da ita baya dana sanin auren ta kamar yanda yayan sa yake dana sanin auren mariya, bashi da buri a yanzu kamar ya dauwama da Halima cikin farinciki har qarshen rayuwar su.

*

Kwanci tashi yau Ayusha take cika shekara biyar da haihuwa, girma take kyawunta yana fita a hankali ba kamar sanda aka haifeta ba, tana da shiga rai duk inda taje ko aka je da ita, bata da hayaniya kamar sauran yara da zaka gani suna rashin ji ko barna, she is always silent wanda iyayen ta basa son hakan, suna so su ganta tana wasa sosai amma sam, she is introvert at her age abun mamaki ne, she feel more comfortable focusing on her inner thoughts and ideas, babu abinda take so kamar zama da iyayen ta biyu kacal rather than her friends ko wani a waje, ko a class bata damuwa da kowa sai dai tayi ta zuba masu ido tana kallon yanda suke wasanni idan babu malami a aji.

Ko a wurin breakfast ita kaɗai take abun ta she dont like anyone close to her.

Idanunta abun sone ga duk wanda ya gani, ba wasu manya bane can amma they are sexy, wasu daga cikin malamanta suna kiranta Ayusha Almond, Ayusha Sexy Ayusha Golden, sunaye daban daban.

She feel like complaining to her Dad bata son sunayen amma tana jin nauyin buɗe baki tayi masa dogon bayanin da take gani zai fahimta, kawai tace Daddy sunayen da teachers ke kirana a school bana so kace su daina... zancen yayi mata tsawo da yawa, tasha gwada son yin magana sai tayi shiru gashi tana nanata maganar a zuciya amma a zahiri bata iyawa.

Duk abinda za'a mata ko a gidane bata magana sai dai ta zuba maka idanunta tana kallon ka wanda hakan ba qaramin ƙona ran Halima yake ba a tunanin ta Ayusha wawiya ce ko sakarya da bata iya depending kanta a ko ina, bata surutu babu hayaniya musamman idan zaka saka mata cartoon ta zauna tayi ta kallo.

Ƙarin damuwar su idan abu yana damunta ko tana son ayi mata wani abu ko rashin lafiya shima bazatayi magana ba ta nuna tana so, kukan banza da yara suke yi sa'o'in ta idan ta tashi yin abunta zama zatayi tayi ta hawaye, tanayin mai qara amma ba ko yaushe ba, suka tambayi kansu ko dan tana da halitta biyu ne take yin abubuwa daban dana sauran mutane?

Abu ɗaya ne bata rejecting wanka, bata gajiya da faɗin ayi mata wanka tana son wanka tana son tsabta, idan fitsari tayi ko kashi shima bata qasa da gwiwa wurin faɗa,
'Mamee kizo ki wanke min....shikenan bazata qara magana ba zatayi ta tsayuwa tana jiran mahaifiyar ta.

Kacokan suka ɗauke ta zuwa asibiti domin a duba lafiyarta dana kwakwalwa duk wani bincike ya tabbatar da yarinyar tana lafiya, hakan bai saka yazeed amincewa ba har sai daya ɗauke ta zuwa babban asibiti National Hospital Abuja.

Suma suka tabbatar mashi da lafiyan ta ƙalau kawai nature ne na kowane ɗan adam, kuma kowa da kalar halittar shi, she is introvert meyiwuwa idan ta girma ta sauya ko kuma akasin haka su cigaba da yi mata addu'a.

Fannin karatun islamiya tana qoqari sosai kuma inda bata iyaba ta kan tambayi iyayenta su gyara mata hakan yana saka su farin ciki ganin ba boko kawai take da qoqari ba harda na islamiya kuma kamar tafi bada qarfi a can.

A wani dare suna kwance Halima ta dube sa, tace Ayusha ta shekara biyar ko ka manta da zamu kaita asibiti domin gwaji.

Yace ban manta ba, abu ɗaya ne zuwa biyu, Na farko ina tsoron muje a gwada a same ta ba mace ba bayan kowa ya san ita macece ce taya zamu dawo da ita namiji? Na biyu ni nafi son kasancewar ta a mace shiyasa bana son zuwa na kaita asibiti, kinga komai na mata tana dashi fuska, murya da ɗabi'un ta bata da wata hayaniya irin ta maza da zaki gansu da ƙiriniya.

Tayi ajiyar zuciya kafin tace zuwan mu asibiti yana da amfani Alhaji idan muka barta ta girma a hakan wane namiji ne zai zauna zaman aure da ita da halitta biyu? zata zamo abun gudu da ƙyama a gurin sa sannan ko ka tuna likita ya gayamana rashin yi mata aiki kan iya haddasa abubuwa da yawa, daga ciki akwai ta taso tana mace amma hormones ɗinta na namiji ne bazata iya haihuwa ba ko kuma tazo babu qirji, ka haqura muje asibiti da ita gobe ko zuwa jibi idan Allah ya kaimu zasu bamu zabi ne kaga sai ayi aikin acire gaban namiji mu barta a mace saboda kaga fa gabanta na namiji shima yana da girma zo ka gani, ta faɗa tare da buɗe masa ya gani.

Yayi mamakin yanda yaga gabanta dole ba yanda ya iya ya gyaɗa kansa tare da faɗin shikenan ba damuwa Allah ya kaimu sai muje su duba su gani.

Washe garin ranar suka je da ita asibitin da aka haifeta bayan an ɗauko file likitan ya duba sosai sannan ya tura su wajen gwaje gwaje, basu sami Dr wahab ba an canza mashi wurin aiki shiyasa suka ɗan wahala, yawon gwaje gwaje da suke ya sakarwa Ayusha zazzabi mai zafin gaske bata taba wahala irin na yau ba suje nan a tura su can abu irin na asibitin Uduth, wani result ma sai gobe zai fito bazasu same shi ranar ba.

Haka suka dawo gida ba dan sun so ba, aka bata magani da abinci ta kwanta sai barcin gajiya duk suka zuba mata ido cikin tausaya mata.

Allah ya kawo ƙarshen wahalar nan ki huta muma mu huta.

Bayan kwana biyu sun kammala duka gwaje gwajen da aka basu suka je suka sami likita, abinda ya faɗa masu ba qaramin tada hankalin su yayi ba matuqa, hormones na namiji yafi yawa ajikin Ayusha akan na mace.

Sam bazai yarda da hakan ba ya girgiza kansa cikin tsananin tashin hankali, sai dai na canza asibiti na koma wata ko kuma na fita da ita wata qasa daban da za'a mata aiki a barta mace ɗin ta, sam wannan ba namiji ba ne.

Duk inda zakaje a faɗin duniyar nan abunda na gayamaka shi za'a sake faɗa maka ku yarda ayi mata aikin a barta namiji, HUKUNCIN ALLAH baa jayayya dashi, kuyi addua ku sami wata haihuwar idan kun dace Allah zai baku mace da kuke so.

Mtsew....yazeed yaja dogon tsaki tare da tashi ya soma harhaɗa takardun daya zo dasu ya dubi matarsa cikin bacin rai,

Ke ɗauko ta mu tafi wannan da alama bai san aikin sa ba, nayi baqin ciki da ban sami likitan daya fara duba mu ba.

Halima ta dube shi tace, kayi haƙuri ka zauna yayi mana bayani mai kyau meyiwuwa akwai wata mafita idan kuma babu muyi haƙuri da HUKUNCIN ALLAH kamar yanda ya faɗ...

Zaki tashi mu tafi ko zaki zauna kina rera waƙa ne gaban wani namiji? Jin wannan kalaman nasa ya saka ta tashi ba shiri ta ɗauki Ayusha suka bar office ɗin.

Kwana biyu da faruwar hakan suka nufi Abuja, maganar da wannan likitan ya faɗa na sokoto shi aka sake maimaita mashi amma har lokacin bai gasgasta zancen su ba, shi yana ji ajikinsa akwai wata hikima ta ubangiji dake boye wacce kowa ya kasa gano ta, tabbas Ayusha mace ce kuma a hakan zata girma ta rayu tayi aure har ta haifa masa jikoki.

Sun daɗe suna jayayya tsakanin likita da yazeed kafin daga bisani likita ya bashi last option wanda yana da tabbaci ga hakan, yace kuje kuyi mata kaciya idan ta warke ku dawo da ita, idan abunda zamuyi mata ya nuna namiji ce dole sai dai kayi haquri in har ba kanaso yarinyar ta tashi da halitta biyu ba.

Yazeed yayi jim kafin yayi magana cikin sanyin jiki na yarda da hakan za muyi mata mu dawo kuma zan karbi HUKUNCIN ALLAH da hannu bibbiyu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 23, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now