Babi Na 17-ZEE YABOUR

2.1K 169 6
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        Al’kaluman marubata

   KUNGIYAR:-
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(home of expert and perfect writers)

*TARE DA AL KALAMIN*

*ZEE YABOUR*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

_.......MABUD'IN WAHALA_


*01*

     "Rahma kiyi sauri mu tafi, kaina ciwo yake jarabawar yau ta caza mun brain", Cewar matashiyar budurwa sanye da uniform na makaranta, " Sister ina zuwa zan karb'i sak'o wurin Amina", Ta yatsina fuska alamar gajiya, Kallo d'aya zaka mata ka fuskanci tana da sanyi, sam bata son rigima da hayaniya.

    Kusan minti 5 tana tsaye, ta koma zaune kan dutsen dake bakin gate na makaranta, "Yi hak'uri na b'ata miki lokaci, kayan da zan saka birthday Sophy na aro", " Ke wai bakya gajiya da aron kaya ki saka wanda Allah ya baki, party ma bai kamata kije ba", "Ni bana son haka, ba ruwanki dani", Taja bakinta tayi shiru, tana mamakin hali na Rahma da shegen son k'arya.

    Suna tsaye bakin titi suna taron Napep, wata mota mai azabar kyau k'irar Benz tayi parking saitin su, Rahma tace " Wow Benz ", Sameerah ta kawar da kai gefe, Ya saukar da glass, Matashin saurayi ne mai kyau Dan' gayu, yana sanye da English wears, " Yan mata ina zaku?", Da sakin fuska Rahma tace "Unguwar Liman cikin City", " Ku shigo na rage muku hanya", Tana washe baki tace "Toh"

     "Sister zo mu tafi", " Ki tafi ni zan hau napep", Bata tsaya wata magana ta bud'e gaban mota ta shige, dama bata so ya ganta, Yace yana so, sau da yawa Sameerah ake cewa ana so, abun na mata ciwo.

     "Nan zaki bar yar'uwar taki", " Barta ta cika mugun hali", Yayi murmushi, yaja kan mota, ya hau titi yana ba motar wuta, sautin kid'a na tashi, Rahma nata jijjiga kai tana bin wak'ar, Ya kalleta yace "Ashe kin iya", " Sosai ma", "Ko na kashe ne ki mana", Tayi dariya tace " A'ah"

     Rahma nata satar kallon sa ya tafi da dukkan tunanin ta har suka kawo k'ofar gidansu, ita ta mishi kwatance,

    "Ya Sunan Mallamar?", " Rahma", "Suna mai dad'i, Am Lukman", " Sunan ka mai dad'i", Yayi murmushi yace "Ko zaki bani number wayarki?", Babu musu ta karb'i wayarsa k'irar IPhone 11pro max ta saka masa, " Sai na kira ki", Ya fad'a yana kashe mata ido, Fuska d'auke da murna tace "Tohm nagode", Ta bud'e murfin motar ta fita,

    Ta shiga gidansu cike da farin cikin ta samu irin saurayin da take so, Dan' gayu, mai kyau da kud'i.

    Sameerah ta tari Napep, ta shiga cike da takaicin halin Rahma.

    B'angarensu ta nufa, bakin murhu ta tarar da mahaifiyarta na hura wuta, " Gwaggo ina wuni?", "Lafiya lau, an dawo", " Eh Gwaggo nazo miki da labari mai dad'i", "Haba ina sauraren ki", " Na had'u da saurayi mai kud'i, kinga motar sa da wayar sa", Ta ajiye icen data d'auka tace "Da gaske", " Wallahi Allah", "Allah yasa mijin auren ki ne ko ma huta da talauci", " Amin Gwaggona", "Da nayi rawa da juyi", " Ai shine ma mijin", Ta fad'a tana shigewa ciki.

     Sameerah ta shigo gida, lokacin tuni Rahma ta manta da ta kawo, Ta kalleta ta kwashe da dariya, Bata lura da ita ba, Ta wuce b'angaren su.

     Gwaggo tace "Lafiyar ki?", " Sameerah ta bani dariya, wai fah k'in shiga mota tayi ita ustaziya", "Gulma dai, ustaziya a ina, ki fita batun ta, ga dukkan alamu yarinyar bata da k'ashin arzik'i, ki duba yaron da take kulawa", " Gwaggo ai tana bani mamaki, ni wallahi ko a k'afa aka d'aura mun shi sai na k'wance", "Ke kinyi gadon arzik'i ai", Haka suka cigaba da kushen Sameerah,

    Kwance kan ledar dake tsakiyar falo ta tarar da Mahaifiyar ta, " Umma lafiya kika kwanta k'asa", "Kwanciyar k'asan naji tana mun dad'i", Tace " Sannu ya zaman gida?", "Lafiya lau", " Ina su Khadija", "Sun tafi islamiyya", " Yau bazan iya zuwa ba na gaji sosai", "Ai kun kusa gamawa, yaushe zakuyi ta k'arshe?", " Gobe ", " Allah ya bada nasara", "Amin"

    K'uryar d'aki ta shiga, ta tub'e kayanta, Ta fito da d'aurin gaba da hijab, saboda samarin gidan, Ta d'auki bucket, ta d'ibi ruwa a rijiyar gidan, Ta nufi bandak'i dake tsakar gida, Wanka tayi,

    Mai da turare kad'ai ta shafa, ta saka doguwar riga, Ta kwanta kan katifa, Bacci ya d'auketa.

     Atiku Mai goro dattijan mutum ne, mutumin arzik'i, Yana da rufin asiri dan ba za'a kira sa mai kud'i ba, Matansa Biyu Hansatu da Lami, Yaransa 7, Hansatu nada 4 Jabir, Lawal, Safara'u da Ummul khairi, Lami nada uku Sabi'u, Yahuza da Safiyya.

     Jabir, Lawal, Sabi'u da Yahuza duka sunyi aure, Atiku a cikin gidan sa, yama kowanne b'angaren sa, Safara'u, Safiyya  da Ummul khairi suma sunyi aure anan cikin garin Zaria.

    Gidan ya zama babban gidan(Family house), Ya cika da yara da jikoki, Sabi'u shine mahaifin Sameerah itace yar'sa ta farko da k'annenta biyar, Shekararta 17 tana matakin k'arshe a sakandire, Rahma yar' Lawal ce itace ta uku a wurin iyayenta Tana da yayye biyu maza, Sa'anni ne da Sameerah.

    Kunsan duk inda akace gidan yawa, ba'a raba sa da tsegumi, hassada da gulma, Toh hakan take a gidan mai goro(Kamar yadda ake kiran gidan), Burin kowacce taga tafi d'aya, ko yaranta sunfi, Yayen Hansatu da Lami suna kishin yan'ubanci, Matansu duk da kasancewar su ba kishiyoyi ba suna kishin sauri.

     Mahaifiyar Sameerah Allah ya zuba mata hak'uri da kawar da kai, Ita Sameerah ta gado, Taba yaranta kyakkyawan tarbiya, Basu taso da halin k'in Yan uwansu ba, kowa da zuciya d'aya suke d'aukar sa, Duk da halin k'iyayya da wasu mutanen gidan ke nuna musu.

   Mahaifiyar Rahma tafi dukansu bak'in hali da nuna tafi kowa da son k'arya, Ta d'aura yaranta kan son abun duniya da tara dukiya, Gata da ganin k'yashi, Tafi kishi da A'i (Mahaifiyar Sameerah) kasancewar tafi duka matan gidan kyau da rufin asiri, Mijinta na matuk'ar sonta yana mata hidima sosai, wannan ya k'ara sa take jin haushin ta.

     *Wannan kenan*

KUNDIN HASKE💡Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin