4

1.4K 152 16
                                    

KUNDIN HASKE

ALKALUMAN MARUBUTA🤝

*💡 HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*

*Wattpad :-AyusherMohd*

TARE DA ALKALAMIN

*Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*MENENE MATSALAR?*

*Babi na Ashirin*

Domin neman Kundin Haske daga na 1 zuwa na 20 ziyarci https://my.w.tt/psg00vI7a5. Ko wani babi yana kushe da labarinsa ne, ba cigaba bane ba kuma a hade suke ba.

Part 4

Aunty Rabi ce ta kirashi yana hanyarshi ta dawowa daga aiki a gajiye yake sai dai ganin tace mahimmiyar magana zasuyi yasa ya wuce gidanta.

Sai daya zauna a falo sannan ta aka sanar mata da zuwansa dan ba laifi mijin Aunty Rabi nada hali sai dai su uku ne a wajensa.

Sai da suka gaisa sannan yace "Yaya Rabi ya akai?"

Kallansa tai tace "Abdul mai zai hana ka dinga ba matarka kulawa ko kadan ne? Zahra na bukatarka."

Yanayin fuskarsa ne ya canza yace "kara ta ta kawo kenan ko me?"

Gaban Yaya Rabi ne ya fadi ba dai garin gyara sun ballo wani abin ba?

Da sauri tace "wani irin kara kuma Abdul? Magana dai zamuyi ma fahimtar juna."

Shiru yai har Yaya Rabi ta gama magana bai kara tofawa ba, mikewa yai bayan ta gama ya mata sallama ya fito.

Hankalin Yaya Rabi ne ya tashi dan yanayinsa yasa ta fahimci tabbas sun kara balle lamarin, waya tawa mai gidanta ta sanar dashi.

Fada ya hau ta dashi yace "akan me zaki kirashi? Me yasa wani sa'in ku mata bakwa lissafin yanda namiji zai ji? Harkar gabanku da damuwarku kawai kuka sani?"

Tace "bari na kira Zahra."

Zahra kam a lokacin tana alwala a toilet wayar tata kuma tana falo, tana fitowa ta tada sallar magrib a daki, zama tai tana addu'oi tare da fatan Allah ya karkato mata da hankalin mijinta.
Sai data shafa sannan ta mike tana ninke sallaya tare da kara kallan agoggo, haryanzu bai dawo ba? Ajiye sallayar tai zata cire hijab taji alamar bude kofa.

Da sauri ta zare hijabin ta fito, Abdul ne ya shigo fuskarsa a murtuke sosai ya wuce cikin daki ba tre da ya ko tanka mata ba.

Biyoshi tai tace "andawo lafiya?"

Kallanta yai sosai yace "karata kika kai gun yayarki?"

Gabanta ne ya fadi, can yaje kenan? Daurewa tai tace "kara kuma Luvly?"

Cikin fada yace "ni danki ne?"
Idanu ta zaro tace "d'a?"
A fusace yace "ko mahaifiyar data haifeni bata taba kai karata gun wasu ba balle ke, ita yayar taki da kika kai karartawa gunta uban me kike tunanin zata min?"

Hankalin Zahra ne ya tashi tace "Abdul ba haka bane." Tai maganar cikin rauni tare da niman rike hanunsa.

Finzge hannunsa yai a fusace cikin tsananin fada yace "ke kike tunanin zaman da nake dake nine nake kwararki? Ni kinga farinciki a tattare da zaman da nake dake? Uban me kike min da zai sani farin ciki?"

Hawaye ne kawai suke zuba a idanunta tace "Abdul duk biyayyar da nake maka?"

Wani kallo ya mata yace " biyayya? Ce miki akai shinake bukata daga gareki?"

Kallansa tai tace "Abdul?"

Wucewa yai toilet a hasale ya banko kofar, zama tai a bakin gado tana zubar da kwala, itakam wani irin rayuwa ne wannan? Meyasa duk sanda take yunkurin gyara auransu sai komai ya sake tarwatsewa? Menene matsalar dake faruwa tsakaninsu?

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now