Shafi na shida

1.4K 113 3
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*

  *shafi na shida*

Fuuuuu sadiya tayi ta wuce cikin dakinta ta bugo kofa tamkar wata kububuwa,kallo mama ta bita dashi ta girgiza kai tana mamakin halin sadiya.....

Ranan wuni sadiya tayi a daki bata fito ko kofar daki ba ta kunna waka ta cika gidan tamkar studio,sai wajen laasar ta fito ta fara haramar girkin dare tanayi tana girgije girje.....daidai lokacin shukra ta dawo daga makaranta da sallamarta ta shigo gidan,sadiya wadda ke tsaye bakin kofarta ta dago kai ta watsa mata mugun kallo itama shukrar tsaki tayi mata ta shige daki tayiwa mama sannu da gida ta amsa cike da faraa saida ta dan numfasa sanan ta kalli mama tace

"me zaa dafa ne yau mama?inaso in shiga kitchen"

"shukra ai yayanku yace sadiya zata rinka bamu abinci daga yanzun tunda daga bakina sai naki saina bibi koh"

Wani zabura shukra tayi tace "tabdijan mama yanzun anty sadiya zata rinka bamu abinci?aiko mun banu domin na tabbata watar ramewarmu ne ya kama domin wallahi bazamu rinka ci muna koshi ba"

"haba shukra wace irin magana kikeyi haka?ita da kanta tacewa yayanku zata rinkayin abimci damu shima kuma yayi naam da maganar yaji dadi yanzum idan nace wani abu sadiya zataga kamar wani abun ne daban a zuciyata".....

  Murmushin takaici shukra tayi tace "gaskiya mama sanyinki yayi yawa wace surika ce zata zauna surukarta tana yi mata wanan iskancin da sadiya keyi miki tamkar itace ta haifa miki dan?ko da yake dole tayi iskanci tunda taga baba ya rasu inda mai gidan na nan bata isa ba,amma mama dan allah inaso ki rinka gwada mata iya karta"

  "shukra ko ban gwadawa sadiya iyakarta ba allah yana ganinta kuma zataga karshen dik wata fitsara da rashin kunyarta zatazo karshe idan banida hakkinta wallahi bata zama lafiya"

  Haushi ne ya kama shukra batace uffan ba ta gyara kwamciyarta ta lumshe idanuwanta tamkar mai barci....

Karfe biyar nayi abubakar be bari karfe shidan da ya saba dawowa yayo haramar gida saboda kosawa da yayi ya dawo gida ya ga sadiya,saboda yadda zuciyarsa ke azalzalarsa da matsananciyar sonta da shaawarta....

Sadiya tattaro kayan wanke wanke takeyi tana fitowa dasu saboda tana sane takiyinsu tun safe ta fito hannunta dauke da tukwane tajiyo rurin mashin din abubakar da sauri ta shiga kwalawa shukra kira...

Shukra!shukra!!shukra!!!

Taki amsata daidai nan abubakar yayi sallama..."shukra tunda bazaki wanke wanken ba bari inyi abuna tunda tun dazun nake fama dake,dame zanji gashi tun dazun nake faman aiki"

A fusace abubakar ya daga labule babu ko sallama mama firgigit tayi ta dago kai tace "ah ah abubakari yaushe ka shigo?"

"tun dazun na shigo sadiya na kiran shukra taki amsawa saboda iskanci bansan inda ta koyo rashin mutunci ba"

  Gyara zama mama tayi "wani irin rashin mutunci kuma abubakar?"

  "Idan ni nakirata ai bazatamun haka ba amma matata nakiranta tana jinta taki amsawa saboda rashin mutunci,to wallahi zanyi maganinki,maza ki wuce ki dauraye mata kwanuka"....

Mikewa shukra tayi kwalla ta ciko a idanuwanta nan da nan ranta yayi matukar baci tunda take da yayanta bai taba gaya mata bakar magana ba balle yayi mata cin mutunci....

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now