Shafi na biyu

3.3K 306 2
                                    

KUNDIN HASKE

            Al 'kaluman Marubuta

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
          Fertymerh Xarah💞

HANGEN NESA.....

     
BABI NA BIYU

Shafi na biyu...

'Ko da ya dawo gida bai mata magana ba amma har a xuciyar sa abin ba qaramin qona masa rai yayi ba.

Yana kwance cike da tunani iri iri ta shigo,

Ta xauna tana fadin, Aliyu dama wannan material dinne nake son ka dinka min irin sa, kudin sa baxai wuce dubu takwas ba duba ka gani.

Kallon ta yayi batare da ya dubi material din ba, yace bani da kudi baxan siye ba.

Tayi murmushi tana fadin, idan ka samu nake magana ai nafi kowa sanin kai kullum baka da kudin, ina ji ai an kusa maku albashi ko?

'Ko anyi albashin baxan siye ba ko dole ne,

Ta saki baki tana kallon sa,

Wai meke damun ka, kaje an bata ma a waje xaka xo ka sauke fushi akaina, akan wane dalili?

Ni xaki wulaqanta Safiya, in siyo maki abinci ki dauka ki kaiwa mahaifiyata, wato ita ce mai cin dawa saboda kin raina min mahaifiya.

Tace au, shiyasa kake wani tada jijiya haka ashe dan na kyautar da dawa ne, to miye aciki, lada xaka samu kuma ga albarkar iyaye.

Yace ke meyasa baki dauka kin kaiwa iyayen ki ba, ko ke bakya neman albarkar su ne.

Tace saboda basa cin dawa,, ni tun da na taso a gidan mu ban taba ganin ta acikin gidan mu ba.

Yace to shikenan, xakiyi nadama yasa kai ya fice.

Tabi bayansa da kallo tana harara kafin ta tabe baki haka kawai baxan xauna na cutar da kaina ba, idan banji dadin rayuwa a yanxu ba har sai yaushe xanji.

Yana fita ya sami guri ya xauna, wayar sa ya ciro ya kira kuluwa, yarinyar da yake so a yanxu, nutsuwarta da kyawawan halinta suka sanya yake ra'ayin ta har yake burin auren ta,

Kasancewa da ita a waya yaji duk wani bacin ransa ya kau har ya manta halin da yake ciki, ko da ya gama wayar ya shiga cikin gida bai bi ta kanta ba, yaransa kawai ya duba yayi kwanciyar sa.

'Washe gari bayan fitar sa ta nufi inda Bilkisu,

Wai Aliyu jiya sai gashi ya siyo min dawa nayi masa girki da ita, kiji fa.

Bilkisu tace to menene laifi aciki, ya siyo abinda yake so ya kawo gida a girka masa,

Aa wallahi haba dai, bai siyo abin kirki ya kawo ba sai dawa, sai kace bashi da kudin da xai siya mana abinci mai dadi.

Safiya kiji tsoron Allah duk qoqarin Aliyu akan ki bakya gani sai hangen na wasu, shekaranjiya kika gama fadin alherin da yayi wa iyayenka, da na gaya maki abinda nawa mijin ya yiwa iyayena kika xo kina xagin sa wai baiyi qoqari ba, haba idan baki gode masa ba ya kike so yayi, arxikinsa ba daya da mijina ba ya kamata ki gane bafa dole duk abinda aka yiwa wata ba kema kice sai mijinki yayi maki, dan Allah ki gyara rayuwar auren ki, wallahi ko wacce mace mutuncina gidan auren ta ne.

Safiya taja numfashi kafin tace maxan nan baxaki gane kansu ba tukunna, suna da kudi amma sun fi so su quntatawa iyalansu.

Bilkisu ta katse ta tana fadin idan kika ce haka baki Ma aliyu adalci ba, duk qoqarin sa akan ki, wallahi kiji tsoron Allah kisan me kike yi, jiya da na gayamaki babana ya siya min telan dinki kinje kin sami mahaifin ki ya siya maki?

Tace saboda me xance ya siya min?

Tace to saboda me xaki riqa tirsasa aliyu ya siya maki abubuwan da bashi da qarfi akan su, abinda duk kika samu kiyi haquri da shi ina gayamaki gsky ne.

Safiya tace to nagode,

Bilkisu ta tashi tana fadin ni har kin samin kwadayin tuwon dawa, shi xan yi yau kuwa, oga ma xaiji dadi nasani.

Yana cin tuwon dawa ne, Safiya ta tambaya,

Sosai ma kuwa, duk abinda na girka masa so yake haka duk abinda yace na masa ina masa dan farin cikin sa.

Suna haka mijin bilkisu ya dawo, sai ga yara suna shigowa da kayan cefane, su arish, doya, cabbage, kwalin exotic, harda su malt, Safiya sai ware ido take tana kallo.

Lallai cabdi duk wannan kayan sai kace gidan wani hamshaqi.

Yana shigowa suka gaisa, ta bar gidan.

Bata jima da komawa ba mahaifiyar ta taxo, dama aliyu yaje ya kai karar tane akan a mata magana ta sauya, dan yana sonta kuma gwargwado yana iya qoqarin sa akanta.

Fada sosai mahaifiyar tayi mata tare da tunasar da ita asalinta domin su kansu ba masu kudi bane kuma abincin da take wulaqantawa ko su suna neman sa.

Bayan tafiyar mahaifiyar ne da magrib sai ga yaro yaxo da abinci a cooler wai inji Safiya.

Tana dubawa tuwan dawa ne yaji nama sosai sai qamshin man shanu ke tashi,

Ta xauna taci sosai sai santi take ashe tuwon dawa Ma iya ne musamman idan ya sami kayan gyara, lallai kam dole xata lallaba aliyu ya siyo mata dawar tana so tayi irin sa.

Yinin ranar aliyu bai dawo ba sai dare yana inda mahaifiyar sa, bai damu da ko tayi girki ko bata yi ba,

Babu sannu da dawowa ko ya aiki sai ta soma fadin,

Kowane magidanci idan xai shigo gidansa xaka ganshi da cefane masu yawan gaske, irin su kwai, dankalin nan na turawa, doya, kayan marmari da sauran su saboda su farantawa iyalansu amma kai aliyu sam ba haka kake ba, kai kullum kace babu sai kace akan ka aka fara babu a duniya, haba kaxo ka gyara rayuwarka yanda xa muji dadi mana.

Shiru yayi mata baice komai ba,

Ba kunya tace gobe kaxo min da dawa, ina sha'awar naci tuwan dawa.

Kallon ta yayi, kafin yace bani da kudi in ma akwai sai dai na siyo na kaiwa tsohuwa saboda neman albarka.

Tace wai maganar nan bata wuce bane nifa tuni na barta, saboda naga kana ta fushi dani ya saka xan yi ma na faranta ma, kayi haquri kaji aliyu na.

Tabe bakinsa kawai yayi ya shige toilet abin sa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now