Shafi na biyu

2K 162 6
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


2


Bude IG din tayi ta shiga DM din, "Really" shine reply din da yyi mata, ta mayar masa reply ita ma tace "You reason it...." Xata ajiye wayar sai ga message dinsa yace "Ok then" turo baki tayi ta rubuta masa "Reply my salam now" bayan kusan minti daya ya turo mata message da "Wslm" bata san lkcn da wani murmushi yyi escaping lips dinta ba, sai ta rasa me xata kara ce masa, can dai tace "Good" bai sake mata reply ba, ta mike ta fita xuciyarta fes. Karfe goma ta gama gyara gun kwanciyarta ta dauko wayarta daga caji kasancewar akwai wuta, ta kwanta dai dai nan kiran Umar ya shigo wayarta, tsaki ta yi kawai ta daga kiran, da damuwa yace "Are you okay Fatima, I've been calling tun jiya you are nt responding" murya can kasa tace "Bani da lafiya tun jiyan" yace "Subhanallah, what's wrong, me yake damun ki" yamutse fuska tayi tace "Xaxxabi" yace "Ya salam, kun je asibiti?" Tace "Eh mun je" yace "Amma da sauki yanxu?" Ta tabe baki tace "Shi yasa na daga kiran" yace "Toh Allah ya kara lafiya gobe xan xo da safe" a takaice tace "Toh" yace "Ya su Ammi?" Tace "Lafiya" yace "Toh shkkn ki kwanta my dear, Allah ya sauwake, I will cal tomorrow" tace "Toh" kafin ya kashe wayar ta kashe sannan ta kunna data, ga mugun mamakinta sai ta ga follow request din Elbash don ita ma private ta mayar da account dinta duk da ba ta taba sa hoton ta a IG ba sai hotunan kananun yara masu kyau followers dinta sun kusa dubu takwas, and she is just following few, ta wara ido cike da farin ciki ta yi accept dinsa, tayi ta jira taga ko xai mata magana amma shiru, tana son tayi DM dinsa amma ta kasa don bata ma san abinda xata ce ba, can dai ta daure ta tura masa message kamar haka, "I am Fatima Muhd the daughter of the former minister of Education in Nigeria, am studying pharmacy at Cambridge uni, currently home for holiday, what more...." Bayan kusan minti biyar ya turo mata message kamar haka
"Is there any need of what I didn't ask?" Xaro ido tayi ganin abinda ya turo mata, ji tayi kamar kasa ya bude ta shige, ta cije lebe gwiwarta a sake ta mayar masa reply "Mtsww na fi karfin ka min wlknci malam don na fi ka nesa ba kusa ba, I pinged you for a purpose.... dat aside da baka kai matsayin inyi following ka ba bare in fara maka introduction, who did you think you are?" ta murguda baki ta tura masa bayan ta gama typing din, ba a dau lkci ya mayar mata reply kamar haka "Really?" tace "Yes" ya bude message din sae dae bai yi reply ba ta yi ta jira amma shiru har ta fara jin bacci, ta kashe data rai ba dadi ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa. Washegari da ya kasance laraba har kaninta suka tafi makaranta bacci take, Ammi kuma bata tasheta ba tana ta aikace aikacen gida, sai kusan karfe goma ta tashi ta fito waje ta Debi ruwa a rijiya don yin wanka, sai da ta fara wanke baki sannan ta shiga wankan, ta dau lokaci tana shafe shafenta ta fiddo atamfarta ta saka kasancewar ranan juma'a ce sai a sannan ta fita ta shiga dakin Ammi ta ganta tana karatun al-qur'an, ta bude cooler da ta gani a rufe taga kunu ne sai kosai dake cikin leda, tasan nata ne, ta yamutsa fuska ta juya ta koma dakinsu, wayarta da tayi plug da Asuba a charge ta cire, ta bude data, still tayi tana kallon message din Elbash... "Send your face" Bata san lkcn da ta fashe da wani dariya ba, tana murmushi ta rubuta masa "For what?" Ashe yana kusa sai ga shi ya mayar mata yace "I don't chat with people i don't knw facially" wani murmushin tayi tace "I don't think that bunk policy of urs is true coz u have been chatting with me since yesterday" ya mayar mata da cewa "And What are you insinuating?" Ta fashe da dariya tace "What you are thinking ryt now" yace "Are you calling me a liar?" Ta wara ido tace "Is that what you were thinking, ohk then so be it, that was what I insinuated" Yace "How dare you" ta tura masa emoji din dariya tace "Whatever" yace "Ohk xa ki gane baki da wayo" ta tura masa da cewa "Babu abinda ka isa ka min malam, ni ban ce xaka gane baka da wayo ba sai kai?" Yace "Ohk" ta tura masa da gwalo da dariya, ya bude bai ce komai ba, ring din wayarta ya sa ta tsaida dariyar da take, Umar ne ke kiranta, ta hade rai ta daga, yyi sallama yace "Kin tashi lafiya dear" kamar ana tilasta ta tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau ya jikin?" Tace "Na ji sauki" yace "Xan je kasuwa ne na biyo in duba ki am outside yanxu" tace "But is there any need?" A hankali yace "There is pls Fatima" ta tabe baki tace "Gani nan xuwa" daga haka ta katse wayar ta mike ta dau gogaggen Hijab dinta ta saka ta fita xuwa dakin Ammi, durkusawa tayi gefenta tace "Ina kwana Ammi" bbu yabo babu fallasa Ammi ta amsa, tasan laifinta daya bata tashi da asuba ba yau duk da bata sallah, a hankali tace "Ammi Umar ne ya xo yana waje" Ammi tace "Ya rage naki kuma" ta yi shiru kafin ta mike ta fita, yana tsaye jikin bango ta samesa, Sanye yake da shadda fara kal da hula, Umar xa a sa shi a sahun handsome guys, he is handsome, kana ganinsa ka ba bafillatani da tsayinsa, a Kano yyi Bsc dinsa a fannin Biochemistry, yyi masters kuma a medical Biochem, aiki da bai samu ba tukun yasa yake kasuwancinsa a nan Suleja don family house dinsu na nn, sun hadu da shi ne tana ss1 lkcn ma bai gama karatu ba, ita kanta tasan son da Umar ke mata ya wuce misali ita ma a da tana sonsa sosai amma tunda taga kalan motar saurayin sa'adatu taji duk duniya bbu wanda bata so kamar shi, a da bbu wanda ke mata kyau a maxa kamar shi, amma tun da Husnah ta fara nuna mata wayayyun maxajen IG taga ashe ba ma shi da wani kyau, Elbash ya fi sa kyau da wayewa nesa ba kusa ba, ta turo baki ta rungungume hannu tace "Gani" a hankali yace "Ya jikin?" Tace "Na ji sauki" yace "Allah ya sauwake, ya Ammi fa?" Tace "Tana lafiya" yace "Toh ki gaishe min ita, Xan fita kasuwa ne, just want to check on you" tace "Nagode" dubu biyu ya ciro ya mika mata yace "i wanted getting some fruits for you but it's too early ba su fito ba, gashi ki aiki su Ummi su siyo maki anjima" tace "A'a ka barsa naji sauki ai, thank you" yace "No take it pls dear" ta d'an yi jim kafin ta risina ta karba tace "Nagode" yyi murmushi yace "No thanks baby" juyawa tayi tace "Sai anjima" daga haka ta shiga gida, sakonsa na gaisuwa kadai ta ba Ammi sannan ta wuce dakinsu ta boye kudinta. Bayan an sakko sallar Juma'ah fatima tace ma Ammi xata je gidan wata kawarta da tayi aure Safia, da kyar Ammi ta bari taje kasancewar bata barta taje bikin ba sbda su Husnah, hijab dinta har kasa ne jikinta ta fita gidan sakale da jakarta, ta samu adaidaita ta hau, tana kallon suka wuce hanyar gidan Safia ta turo baki ta kauda kai, sai da ta kai inda xata je ta fito ta basa kudinsa ta shiga gidan, duk da kasancewar gidansu d'an karamin gida da mahaifinsu ya rasu ya bar masu gidan ya fi na su Husnah nesa ba kusa ba, Tsakar gidan kaca kaca ga kwanuka da kaya ta ko ina, Inna mahaifiyar Husnah na xaune tsakar gida tana yankan awara dafaffe, ta duka har kasa ta gaisheta, ta washe baki tace "A'a Fatima daga ina haka" tace "Daga gida Inna" Inna tace "Ikon Allah, Ya su Amina?" Tace "Suna lafiya inna, Husnah na nan?" Tace "Wllh kinga tun safe ta fita ban ma san inda tayi ba, amma nasan baxata wuce anguwar nan ba, ki kira lambarta" nace "Toh" tace "Ki shiga dakinsu ki xauna" mikewa tayi ta nufi dakinsu Husnah na shiga, ita dai tasan a responsible rat will not live in that room don bayan datti, untidiness har da wari yake, ta raba na xauna gefen katifarsu da yyi dukun dukun ta shiga kiran layinta kasancewar tana da sauran bonus, bugu biyu ta dauka tace "Mara kirki sai yau xa ki kirani bayan ko asi bani da shi tun ranan da na bar gidan Ku" Fatima tace "Ke ina fa gidanku ina kika je?" Tace "Kaji ta, ke din ce xa ki xo gidanmu" Fatima tace "Kinga ni ba wani kati me yawa gareni ba, wllh ba wasa nake ba, Inna tace tun safe kika fita" cike da farin ciki Husnah tace "To to Gani nan xuwa ban yi nisa ba" daga haka ta katse wayar, Fatima ta tabe baki, kafin minti goma sai gata ta shigo dakin ta rungume ta tace "Wayyo Ashe da gaske ne, welcome besty" Fatima na kallonta tace "Ina kika je tun safe" Husnah tayi kasa da murya tace "Kinga saurayin Sajida ne yace xai kai mu outing yau, tun safe muke jiransa har yanxu shiru ni har na fidda rai Wllh kilan ma karya ya shirga mata" Fatima tayi dariya tace "Kuna da aiki, ni ba wannan ba, kinsan wnn Elbash din yyi following dina back har mun yi chat" Husnah ta xaro ido tace "Kice Wllh" Fatima ta fashe da dariya tace "Wallahi" wani uban tsalle ta doka tace "Bani in sha kawata, garin yaya" Fatima na murmushi ta bata wayar bayan ta bude IG dinta ta shiga DM dinta da Elbash, Husnah ta nutsu tana karanta messages din, lkci daya ta hade rai tace "My God, to ai tsokanarsa kike ta yi Fatima, dubi fa irin maganganun da kike ta gaya masa marasa dadi" Fatima tace "Uhm ai d'an rainin wayo ne shi yasa nake basa amsa dai dai shi" Husnah ta dafe kai tace "No that was not our plan fa besty, ke da xaki dinga lallabasa" Fatima tace "Tabdi, ya raina ni kenan, ke bari kiji yanda yake jin kansa fa nima haka nake jin nawa kan" Husnah ta fashe da dariya tace "Ke a wa" ta hade rai tace "Ni a mutum" Husnah tace "Yanxu har yace ki basa photo ki ki, haba Fatima you want to spoil d plan kenan" Fatima tace "Ke dadi na da ke baki da jan aji wllh" Husnah ta saki baki tace "Jan aji a wannan xamanin, ai kam xa ki ja har ya tsinke Wllh" Dariya Fatima tayi tace "Koh" Husnah tace "Wllh da gaske, yanxu don Allah ki tura masa hoton" Fatima tace "Tabdi bayan nace masa A'a" Husnah tace "Wllh sai kin tura, to don me dama nasa kika yi following dinsa tun farko" daga haka ta dau waya tace "Bari in duba gallery din muga ko akwai hot pics" tabe baki tayi bayan ta dudduba tace "Ba background me kyau a hotunan, jira akwai wata da muka hadu a IG kusan shekara daya kafin wayata ta lalace, yar masu kudi ce Wllh, idan kika ga gidansu sai kin yi suman tsaye, kinga irin flowers da motocin gidansu kuwa, kusan duk sati sai na je gidan Wllh, amma fa da nisa daga nan don kusan dari uku ne kudin mota xuwa da dawowa, yanxun ma can xa mu je kiyi hoton har kaya ma xata iya ara maki na sani, Allah yasa kin fito da kudi don ni ko taro bani da" Fatima ta saki baki tace "Husnah???" Mikewa Husnah tayi ta dagata tace "Dallah muje kada yamma yyi" daga haka suka fita tace "inna bari mu je gidan wata kawarmu mu dawo yanxu" Inna tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, A kula da titi, Fatima kar fa ki wuce daga can ki dawo ki kai ma mamarku awara" Fatima tace "To inna na gode" daga haka Husnah ta ja ta suka fita gidan xuwa inda xa su hau mota.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now