2

1.6K 188 15
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        _*Al’kaluman marubata*_

   *KUNGIYAR:-*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(home of expert and perfect writers)_

_TARE DA AL KALAMIN_

*_MAMUH GEE_*

_BABI NA GOMA SHA SHIDDA_

*YIWA KAI*

*2*

Karfe goma Sha biyun Rana aka gama maimaicin dukkanin dramas dinda tayi missing episodes dinsu jiya ta miqe cikeda farin ciki ta nufi hanyar bedroom din Kamal tafara gyarawa.

Tana gama gyara gado ta harhada dakin ta share tayi mopping ta wanke toilet ta kunna turaren wuta kafin tadawo palon.

Kicin tafara zuwa ta Dora abincin Rana kafin tazo tahau gyaran palon tana cikin mopping uncle shamsu yashigo rungumeda amal tana baccinta,

Cikin dariya tace"

Kai uncle shamsu wlh duk ranar da akayi aurenka da Fatima katafi kabarmu bansan ya zanyi da rigimar amal ba wannan kuka da rigima haka wlh gigitani takeyi.

Shimfidar da ita yayi ahankali kan two sitter tareda gyara mata kwanciya Yana cewa"

Anty hafsat aikuwa princess amal dinmu batada rigima kece dai kike ganin rigimarta sbd tana hanaki kallonsu indiyoyinki.

Dariya tayi tana cewa"

Iye su har uncle shamsu yamata wankanta Ashe,
Aikuwa ka ragemin aiki yanzu sauri zanyi na kammala sauran kar maman sadeeq tashigo mu shiririce akan firarmu Dan kuwa yau Kam babu sauki.

Dariya yayi tareda nufar fridge ya bude tareda saka hannu ya dauko ruwan pure water daya ya fasa yasha Yana cewa"

Anty hafsat kenan,
Ni wlh nayi aure gidana kallon series sokakkene babusa a tsarina sbd kawai wannan Bata lokacin dakukeyi ai sai wata Rana a dafa maka kyankyaso ko gizogizo kaci batareda ansaniba tsabar sauri.

Dariya tayi sosai tana matse mopper tace"

Abin naka ya hada da sharri uncle shamsu,
Yanxu wace mace ce zata Saba da kallon dramas kace idan tazo gidanka zaka hanata ai wlh ko maqwaftane saitaje kallo baka ganin ranar Monday idan zaayi tarkon qauna yanda gidan maman sadeeq yake cika da wasu daga cikin matan layin nan
Kuma wlh wasu akwai kallon gidansu kawai kallon ne idan kana tareda Wanda zaku riqa dariya ko ihu tare yafi dadi.

Wani irin dariyar jinjina zancen yayi Yana cewa"

Wlh dukkaninsu mazajen nasu sunga damane Amma wlh matata dai acikin gidana Kuma a qarqashin ikona bazan Dora doka agidana ta takaba musamman wannan ta banxan kallace kallacen nan Wanda zaisa a gidana nida yayana murasa alqibla.

Hakadai kace uncle shamsu Amma dai zamu gani dukda naga fatimar tun ayanxu tana shakkarka.

Wasu ruwan ya qara dauka tareda ficewa Yana cewa"

Nafita zanje family house idan Yaya kamal yadawo kice masa Nazir ne aka sacewa mashin zanje masa jaje shima yakirasa koda awayane.

Ina gaidasu hajiya Dan Allah Kuma inawa malam Nazir jaje Allah ya tsare gaba.

Maida hankali tayi taci gaba da aikinta sai qarfe uku saura mintuna goma tagama aikinta tsaf har girkin ta jera adan madaidaicin dining dinta taje tayo wanka ta shirya cikin riga da skirt na wani black and red drylace  har lokacin amal bacci takeyi Wanda hakan ba qaramin dadi yayi mata ba koba komai tayi ayyukanta hankali kwance.

Tana cikin sallar la'asar amal ta farka tana idarwa ta nufeta tana murmushi cikin tsananin kaunar yarta ta dauketa tana cewa"

Amal baby ta tashi bacci ko,bari muxo muci abinci amal din dady.

Toilet takaita tasake yi mata wanka Suka fito tasaka mata wasu kayan Suka nufo Palo.

Suna shigowa kamal Yana shigowa da sallamarsa.

Wani irin zillo amal din tayi tana miqa masa hannu dukkanin bakinta a bude tana masa Daria kamar zata fado daga hannuwan mamanta.

Cikin tsananin kaunar yarsa da farin cikin ganinta ya miqa hannu ya karbeta Yana mata dariya yace"

Angel Din dady tanason zuwa gurin dadynta...

Karbarta yayi Suka qarasa dining din bayan hafsat ta karbi jakarsa takai daki tadawo.

Cikin nutsuwa tafara zuba masa abinci tana fada masa saqon uncle shamsu na satar mashin din Nazir.

Da kansa yaringa bawa amal din abinci suna wasarsu harta qoshi dakyau kafin shima yaci suka baro dining din still 'yarsa na hannunsa Suka nufi dakinsa ya ajiyeta kan gado tareda Bata kayan wasa ya tube yashiga wanka.

Ita kuwa tana gama harhada gurin ta kalli agogo taga biyar saura mintuna ankusa farawa taso zaunawa Amma sbd kar Kamal yafara mata fada yasa ta daure ta nufi dakinsa Amma rabin hankalinta na palon nan dai ta tayasa shiryawa suna fira sama sama.

Kallonta yayi bayan ya gama shiryawa zai fita zuwa family house
Ayanda yasanta yasan zuciyarta a daidai wannan lokacin Bata taredasu ya girgiza Kai ahankali tareda
Daukar key din motarsa yace"

Ki shirya amal kema ki shirya muje family house muyi musu jajen gaba daya.

Kallonsa tayi zuciyarta na sanyi sbd dai wlh ba haka tasoba tasodai tayi kallonta tun yau da zafinsu basai gobe ta tsaya kallon maimaiciba.

Ajiyar zuciya tasauke jiki a sanyaye tareda miqewa tadauki amal Suka nufi dakinta ta sako hijab red kan kayanta tareda canzawa amal Kaya ta dauko wayarta ta fito.

A Palo Suka samesa Suka dunguma zuwa mota.

A harabar gidanta Suka hade da maman sadeeq data shigo gidan sbd yau tafison su riqa shatawa tare.

Gaisawa sukayi da Kamal harya tambayi baban sadeeq tace baidawo daga tafiyar da yayiba.

Kallonta hafsat tayi tace"

Ina kika baro sadeeq Kuma da yamman nan kika fito?

Wlh yanacan gurin bb maigadi kinsan haryafi sabawa dana barsa gurin baba maigad ko nuhu almajirina yanda kikasan sune iyayen nasa,
Ni wlh har banason nuhu ayi hutu yaje gida kamar na zauce sbd kiriniyar sadeeq.

Ganin zasu batawa Kamal lokaci Yana cikin mota zaune yasa Suka datse hirar harsu dawo.

Tafiyar mintuna ashirin ce takaisu family house dinsu Kamal din inda mahaifinsa da matan mahaifinsa tareda sauran qannensu suke sbd shi dagashi sai shamsu mahaifiyarsu ta Haifa ta rasu.

Koda sukaje Abba na gida nan suka zauna aka ringa jajanta yanda abin yafaru har magriba tayi mazan Suka nufi masallaci matan Kuma suka bada haramar yin tasu.

Basu baro gidanba sai bayan sallar ishai Suka dawo dukkaninsu tareda uncle shamsu.

Koda Suka dawo abinci kawai taci taje ta kwantawarta sbd samun damar tashi da wuri gurin kammala ayyukan abincin safe sbd yanayin aikin Kamal na sammakone sbd banki ne yake aiki.

Washe gari tun qarfe 6:30 ta tashi tafara shirye shiryen breakfast cikin nutsuwa sbd gudun kartayi aikin sauri kamar na jiya yabarta da abincinta.
#mamuhgee

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now