Babi na goma_Slimxy

2.1K 126 2
                                    

*KUNDIN HASKE*

     *AL KA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

     *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSO...* 💡( _home of experts and perfect writers_ )

      *ALKA'LAMIN*
           *SLIMZY✍🏼*

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*

     *shafi na daya*

Tsaye take a bakin kofar dakin yayinda ta kasa kunnenta a cikin dakin datake tsaye,daga inda take tsaye zata iya jiyo sautin tattaunawarsu

"Nidai abubakar banida abinda zance maka sai Allah ya saka da alheri Allah yayi maka albarka yakara budi akan harkokinka,domin a kullum ina alfahari da kasancewarka da' namiji a gareni Wanda banida kamarka babu abinda muka nema muka rasa nikam alhamdulillahi,wanan kudin da kabani inyi Sana'a naji dadinsu Allah yayi albarka"

  Dammm gaban sadiya ya yanke ya fadi take bakin ciki yazo ya turnike zuciyarta a inda take labe tana sauraronsu lallai abubakar wato fifita uwarsa yakeyi akanta?har kudin Sana'a ya dauka yabata ita tana zaune saiya gadama yake bata kwabonsa to wallahi bazata yardaba wanan ai zaluncine ya rika fifita mahaifiyarsa akanta tana cikin wanan tunanin ne muryarsa ta katseta...

"Ameen ummah meye amfanin samun danakeyi inhar kannena da mahaifiyata basu huta sunyi farin ciki ba?a kullum banida buri daya wuce inganku cikin farin ciki da walwala"

  Kara kasa kunne takeyi yayinda gumi ya ke karyo mata a tsaye a bakin kofar,wato abubakar dai kudi ya dauka yabawa mamansa itakuwa ko oho tazama hoto ko tambayarsa tayi saiyace mezatayi dashi saiya gadamar bata yana fifita mahaifiyarsa akanta,lallai wanan bakardagar matar ta zame mata karfen kafa,shiyasa ake cewa gara ka auri maraya daka auri wadda uwarsa keda rai duk tabi ta kalallame komi....

   Tana cikin wanan tunanin tajiyo muryarsa yanawa mahaifiyarsa saida safe,cikin hanzari sauri sauri tabar kofar dakin ta ruga ta shige dakinta ta nemi kujera ta zauna ta cika tayi famm fuskarta daure tamau kamar bata taba dariyaba...

  Da sallamarsa ya shigo dakin,ciki-ciki ta amsa fuskarta a daure,kallonta yayi ya saki lallausan murmushi yasan akwai matsala

  Gefenta ya zauna tare da janyota jikinsa"uwar gida sarautar mata halimatu saadaiya waya taba munke?"

  Kamar wacce aka tsikara ta mike tsaye cike da masifa  tafara magana"ninasan baka sona abubakar tunda ka aureni babu abinda kake tsinanamin kullum sai bacin rai,ga fifiko da kake nunamin na uwarka da yan uwanka sunfini daraja,ka duba kagani tunkarfe nawa naji alamar shigowarka gidan nan banga keyarkaba kana dakin can ana kitsa maka karya da gaskiya,kana dauka har gajiya nayi na biyoka zan shiga dakin kenan naji innah tanayi maka godiya kabata kudi tayi jari,ni tun yaushe nake fama dakai akan kabani kudi nayi jari ka hanani?amma ita ka dauka kabata,wai nikam abubakar innah kishiyata CE?nikake aure ko ita?"takarashe maganar cike da masifa.

   Tunda tafara magana ya kafeta da idanuwa motsin kirki yakasa sadiya na basa mamaki be taba ganin masifa irin wanan ba a rayuwarsa ace sadiya batada wadda take kishi da ita sai surukarta saboda takasa fahimtar innah bata iya zama da surukarta ba,wanan masifa ta sadiya ta ishesa yarasa ta inda zai bullo mata ta fahimci matsayin mahaifiyarsa daban matsayinta daban kullum cikin balai yake da sadiya akan surukarta,dolene ya kiyaye hakkokin mahaifiyarsa matukar yanaso yagama da duniya lafiya amma sadiya idanunta ya rufe nema takeyi tasashi cikin halaka,gumi ne yakara karyo masa babban abinda yake damunsa shine yadda sadiya ta raina mahaifiyarsa Sam bata ganinta da kima da daraja ga kishi datakeyi da ita Wanda ita innah Sam batayiwa sadiyar haka....

   Ajiyar zuciya ya sauke ya kara maida kallonsa gareta sai wani girgiza takeyi tana cika tana batsewa yace"look sadiya nagaji da wanan fitinar taki da wadanan mugayen dabiun naki,ke bakida wata matsala a rayuwarki data wuce mahaifiyata?meta tsare miki?ta rike girmanta bata shiga sabgarki saikece kika dau tsanar duniya kika dora mata saboda son zuciya irin naki,to wallahi kishiga taitayinki baki isa kirabani da mahaifiyataba nafada miki"

   Yana kaiwa nan ga fice a fusace yabarta nan tsaye ya nufi masallaci Dan gabatarda sallahr magriba.

  Fitarsa keda wuya ta shiga kaiwa da komowa ranta a bace jitakeyi kamar ta mutu saboda takaicin abubakar,lallai dole ta mike tsaye akan abubakar tayi sakaci tun farko da batayi maganinsaba ta kyalesa dama kawarta binta ta fada mata zama da suruka saikayi shiri idan ba hakaba kanaji kana gani mijinka saidai ka kallesa gashi kuwa tagani,tabbas maganar binta gaskiya ce dolene ta mike tsaye akan abubakar da mahaifiyarsa dolene ta yanke wanan alakar tasu Dan tanaji tana gani bazata zama yar kalloba komi sai uwarsa saikace wata matarsa?komi ya nema komi ita yana mata biyayya kamar zaiyi mata sujada to wallahi bazata sabuba dolene tasan yadda tayi ta shiga tsakaninsu haka kenan zata haihu itada yayanta su zama yan kallo to bazai yuwuba,dolene ta kawar da wanan shegiyar matar data zame mata karfen kafa.

  Saboda haka takudiri aniyar rabasa da mahaifiyarsa ta karfin tsiya koda makirci koda kissa koda asiri saina raba abubakar da mahaifiyarsa...

*NOTE* _wanan gajeren labarin fadakarwa ne ga matan da suka dauki kishi suka dorawa Kansu akan surukansu mata,akan dik abinda mijinta yayiwa mahaifiyarsa bataso ko kuma tasawa mijin fitina itama saiyayi mata,batare da tunanin cewa ita mahaifiyarsa CE tanada hakkin da zaiyi mata ko menene Dan faranta mata rai dikda kome yayi mata be biyata haihuwarsa datayiba,sai rana daya mace tazo ta nemi juyar masa da kwakwalwa Wanda hakan zaluncine,shaidan yayi tasiri a zuciyar matar tare da zugar kawaye Wanda hakan bedaceba saboda haka mata mufarka mudauki uwar miji a matsayin uwa koba komi ai ita ta Haifa miki da'n kika aura mu kiyaye dan Allah..._

*SLIMZY CE✍🏼*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now