Shafi na uku

2.4K 206 9
                                    

KUNDIN HASKE

AL'KALUMAN MARUBUTAN HASKE

HASKE WRITERS ASSOCIATION

BABI NA GOMA SHA BIYU


*MUTUNCIN MACE........*

*TARE DA ALQALAMIN....*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*Shafi na uku* 0⃣3⃣

*Assalamu alaikum warahmatullah*

*ga masu tambayar farkon kundin haske MUTUNCIN MACE,wato littafi ne wanda yake kaman yadda film episode episode yake,idan wannan marubuciya ta gama nata episode din wata zata kama nata,ga yadda dai abun yake a tsare*

*Babi na d'aya*
*nana d'iso ce ta rubuta shi wanda taken labarinta shine 'YAN ZAMANI*

*Babi na biyu*

*Pherty Xahra ce ta rubuta taken labarinta HANGEN NESA*

*Babi na uku*

*labarin na asmy B aliyu ne mai suna RUWAN DARE(fyade)*

*Babi na hud'u*

*maman khady ce ta rubuta,sunan labarin ABOKIYAR ZAMA(kishiya)*

*Babi na biyar*

*labarin miss xoxo ne mai suna NI NA JAWA KAINA(shaye shayen magungunan mata)*

*Babi na shida*

*marubuciyarsa itace nuceeyluv,sunan labarin nata shine KULA DA MIJI*

*Babi na bakwai*

*zainab bawa ita ta rubutashi,sunan labarin nata TALLACE TALLACE (sanya idanuwa akan tarbiyyar 'ya'yanmu*

*Babi na takwas*

*wadda ta rubuta itace hafsat rano,taken labarin nata shine WAYAR MIJI*

*Sai babi na tara*

*jeddah Aliyyu ce ta rubuta,taken labarin nata HATTARA MATASA*

*Babi na goma kuma*

*Ameena slimzy ta rubuta,sunan labarin nata shine RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

*Babi na sha d'aya*

*khadija ahmad ta rubuta wato kdeey,sunan labarin shine RAYUWAR NI 'YASU*

*SAI NI YANZU DA NAKE RUBUTA BABI NA SHA BIYU DA LABARINA MAI TAKEN MUTUNCIN MACE*

*ina fatan kun fahimta*

*Sauran marubutan haske ma nasu na xuwa xaku same shi daki daki kuma a tsare, ga me buqatar sauran da bai karanta ba ya duba KUNDIN HASKE a wattpad duka xai samu insha Allah*

*KUNDI NE DA BABU KAMARSA,KOWANNE CIKIN LABARAN DAUKE YAKE DA DARUSSA SOYAYYA DA NISHADANTARWA MAI TARIN YAWA*





 

   Washe gari babu inda taje saboda b'acin rai qarara data gani tattare da abban khairat,baki d'aya ya fita a sabgarta,harkarshi kawai yake shi da yaranshi,saidai shirunsa batasan me yake nufi ba,duk da tasan shi sarai,mutum ne wanda baida gaggawar yanke hukunci,yana da baiwa mutum lokaci kafin ya kamashi,saidai kuma kamun nashi bai cika zuwa da d'adi ba,bugu da qari kuma tana tsoron kada ya sake kai qararta wajen malam karo na biyu,don ta tabbatar abin bazai mata da kyau ba,tunda ya mata gargad'i mai matuqar qarfi wancan satin,itakam baki d'aya mamaki suke bata,meye illar ko aibu don ta fita maqota?,ita ba sata ba ba bara ba ba roqo ba ba sane ba,haka kawai a hana mutum sakewa a qunsheka cikin gida,baka da katabus?.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now