Shafi na biyu

1.5K 107 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

*ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

*KUNGIYAR:*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers)*


*AL'KALAMIN*
*SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

*BABI NA GOMA*
*shafi na biyu*

Tana nan zaune tayi zurfi cikin tunanin yadda zata bullowa lamarin abubakar da mahaifiyarsa har akayi sallahr magriba da isha'i ya shigo gidan, karar bude kofarsa ce ta farkar da ita daga tunanin da ta fada,.... Kallo ta bishi dashi ya wuceta ya zauna a kujera ya dauki remote ya canja channel, ita kuma ta mike ta shiga kitchen ta dauko tray din abinci mai dauke da kuloli da jug da kofi ta kawo ta ajiye, plate ta dauka ta zuba mishi abinci sai lokacin tayi mishi magana "abubakar ga abinci"

Ko kallonta beyiba ya maida kansa ga tv ya dauki a akalla 30 seconds ya amsa da ta fidda rai da zai amsa maganarta sanan ta tsinkayo muryarsa yana cewa "nakoshi"

Wani kululun bakin ciki ta hadiye daya taso mata sanan tace"saboda me? "

"saboda haka naga ya dace, ke daga yau ma kada kisakeyin abinci dani na dakin uwata zan rinkaci don banida wadda ta fita"

A harzuke sadiya ta fara masifa inda take shiga bata nan take fitaba "ai abubakar ba sai kace ka dainacin abinci na ba na dakin mama zakaci, sakina ya kamata kayi saika zauna da maman,tunda ta shiga ta fita ta shiga tsakanina dakai burinta ya cika, saboda dai baka son gaskiya? Daga nace ka fifita uwarka akaina sai kace kadaina cin abincina? Ai gaskiya na fada baka adalci abubakar ni a matsayina na matarka baka taba tsinanamun komi ba dik abinda kasamo sai ka shiga dakin ka nuna mata sai yadda tayi dakai to wallahi bazan yardaba matukar kadaina cin abincina saidai ka sakeni".

Tunda sadiya ta soma ruwan masifa abubakar ke kallonta kasa kwakkwaran motsi yayi, ya dauka abin na sadiya na hankali ne ashe ba na hankali bane harda tsantsar hauka da jahilci, idan ba jahilci ba meye nata na hada kanta da wadda ta kawosa duniyar baki daya? Dik duniya kuwa bashida wadda ta fita.... Muryarta ce ta dawo dashi daga tunani

"wallahi bazata sabuba wankan kuturu da sabulu, bazai yuwu inkoma yar kallo ba dan mama bazata koma kishiyata ba inaji ina gani"

"ke sadiya wai dakikiyar ina ce ke? Wace irim dabba ce mara hankali? Ta yaya zaki hada kanki da mahaifiyata uwar data kawo ni duniya har muka hadu na aureki? Inda bata kawoni duniya ba bazaki ganni ki auraba, to bari kiji infada miki dik abinda zakiyi saidai kiyi amma bazan fasa yi wa mahaifiyata biyayya ba"

"ai da ka sakeni ka zauna da ita abubakar"

Shiru mama tayi da kannen abubakar dake kallo a dakin suna sauraren kumfar bakin da sadiya keyi,itadai mama girgiza kai kawai takeyi tana mamakin hali irin na sadiya.... Yar matashiyar budurwar da bazata wuce shekaru goma sha tara ba ce ta fara magana cikin fushi"ni dai mama ya abubakar ya rabu da wanan matar kawai,fisabilillahi mata sai kace kishiyarki mama dik abinda yaya yayi miki sai taji haushi kamar ita ta haifa miki da'n"


Murmushi mama tayi irin na manya "shukra ke nan ke yarinya ce, harabada bazan taba sa dan dana haifa yayi saki ba ko yayi abinda be dace ba, kuyi hakuri yarinta ke damunta zata canja"

"haba mama wanan katuwar ce yarinya? Wallahi koni bazanyi abinda takeyi ba ballantana ita da tayi aure ta mallaki hankalin kanta, dan kawai dai tasamu yaya abubakar din mai hakuri ne sanan kema ta hadu da suruka ta gari inda allah ya hada ta da jarababbun iyayen miji yaushe zatayi wanan, wanan kawai rashin iya zama da suruka ne"

Abubakar ne ya turo kofar dakin a fusace ya shigo da sallama ciki ciki ya nemi kujera ya dafe kansa idanuwansa sunyi jajur saboda tsabar bacin rai cikin fushi ya fara magana

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now