Shafi na uku

3.3K 289 11
                                    

KUNDIN HASKE

            Al 'kaluman Marubuta

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
          Fertymerh Xarah💞

HANGEN NESA.....

     
BABI NA BIYU

Shafi na uku.

Bayan ya fito wanka ya dube ta yana tsane jikinsa da qaramin towel,

Ban gaya maki ba aure xan qara Safiya ina buqatar mace mai sona a yanda nake, wacce ko allura naje na nemo na kawo mata xata karba da murna tana min godia.

Safiya ta tashi hankalinta a matuqar tashe,

Aure aliyu, meyasa? Wlhy ina sonka dan Allah kayi haquri ka yafe min baxan qara ba na daina, dan Allah Aliyu kada kace xaka yi wani auren.

Ya xura doguwar jallabiya yana fadin na dai gaya maki ne na fita haqqin ki, kada kiji labari a gari, aure xan qara yarinya ce qarama mai hankali da nutsuwa, tana da tarbiya idan kin kwantar da hankalinki xaki same ta mai maki biyayya kuma kuji dadin xama.

Ta fashe da kuka mai tsanani, ji take duniyar tana juyawa da ita, Aliyu xai mata kishiya, duk son da take masa baxata iya ganin sa da wata macen ba baxata jure hakan ba, taje tana rarrashin sa da bashi haquri tana kuka, fafur yaqi sauraren ta,

Yace idan kinga na fasa auren nan sai idan bana numfashi a doron qasa ko kuma idan dama Allah ya rubuta cewa ba matata bace, amma ina son kuluwa tana sona, duk abinda xan bata komai qanqantarsa xata karba da hannu biyu tana min godia da addua, amma ke menene bana maki Safiya idan baki xage ni ba ki aibata ni, abinda ake wa wasu matan ba lallai bane ni na iya maki domin hali ba daya ba, kuma ko wane gidan aure da kike gani da kalar matsalar sa, baxaka tara duka jin dadi ace kana da ba, su suna boye maki matsalarsu yayin da ke kuma kike xuwa fallasa na ki sirrin auren mijinki baya maki kaxa baya maki kaxa, na baki ci, sha, sutura da duk wani abu da bai fi qarfina ba amma baki taba gode min sai dai ki aibata abinda naxo dashi ki karba a wulaqance kina hantarata, sai kace ba auren soyayya mukayi da ke ba.

Mata nawa ne a duniyar nan dake gidan aure suke son samun abinda ke kika samu kina wulaqantar wa basu samu ba, mace nawa ce ke auren mai kudi bata sami farin ciki da jin dadi a gidan auren ta ba, mace nawa ce kewa mijinta addua a duk sanda xashi fita ya nemo masu halak, amma ni rabon da kimin addua idan xan fita tun kina amarya Safiya, saboda me baxan nemi na qara aure ba, kwanciyar hankali nake so a rayuwata kuma Allah ya gani ina iya qoqari na akan ki amma bakya gani.

'Dan Allah kayi haquri Aliyu nayi kuskure naga ne laifina wallahi xan canxa, ina son ka aliyu kada ka qara min kishiya ka yafe min, ta kai gwiwowinta qasa tana roqonsa.

Is too late for you baki tashi roqo na ba sai da kika ji xancen kishiya, ki riqe haqurin naki bana so kuma kada Allah yasa kimin biyayya, yayi kwanciyarsa

Daren ranar kasa barci tayi saboda kuka har ciwon kai take ji,

Da sassafe bai bi ta kanta ba yayi shirin sa ya fice, da kyar tayi aikace aikacen da take ta shirya yaran suka yi makaranta, da yake skul din nasu yana cikin unguwar ba nisa da gidan.

Ta nufi gidan bilkisu idanu a kumbure ko xata sami mafita dan ba abinda ta tsana kamar ta wayi gari taga Aliyu da wata mace.

Tun kafin ta qarasa ta jiyo hayaniyar bilkisu tana kuka da alama da mijin nata take,

Menene bana maka Bello, wace kulawa ce bana maka, wane farin ciki ne bana maka, duk qoqari na akan na ganin na faranta ma baka gani duk da haka sai kabi wasu matan a waje, da wannan yawon banxa da kake gwanda ace ka auro matar ka kawo ta nan gidan mu xauna, amma menene amfanin xina.

Yace wai waye ke gaya maki ina neman mata, ni bani da aiki ne sai akan mace, kina maganar komai kina min dan ki faranta min, ni menene bana maki a gidannan dan jin dadin ki.

Ta katse sa tana fadin menene amfanin jin dadin da babu kwanciyar hankali a cikinsa, ka dauki kayan ka da duk abinda kake bani idan xaka bani lokacin ka da kulawar ka, kai nake so ba kayan ka ba, macen da taxo jiya neman ka a tunaninka banji komai akan maganganun da kuke ba.

Yace au ashe labe kike min idan nayi baqi, yarinyar fa yar wajen aiki na ce bilkisu taxo neman taimako bata da kudi.

Taimako xai saka ta biyo ka har gidan auren ka? Tana neman kudi har kuke maganar inda xaku hadu, baxan cigaba da xama da kai a hakan ba, baxan iya xama da mazina ci ba, tabbas xaka sake ni gidan mu xanje yau bello.

Hankalinsa ya tashi yabi bayanta da sauri yana rarrashi,

Safiya dake labe tana ji ta dawo gida jikinta na rawa, ashe mijin bilkisu neman mata yake amma bata taba gayama ta ba kuma bata taba nuna mata ko a fuska ba sai dai ta fadi alkhairi da yake mata, ita kuma kullum tana kan hanyar gayamata abinda Aliyu ke mata.

Taji ta qara son mijinta lallai bako wace mace ke fallasa sirrin gidan ta ba, tana boye damuwar ta da rufawa mijin ta asiri, kome aliyu xai kawo mata xata so sa fiye da ace yana yawon maxa, kuma ba duka mata Allah ke jarabta hakan ba.

Yinin ranar tayi sa gadai tanan ba kuzari, tayi girkinta mai rai da lafiya, ta tsabtace gidan nata sai qamshi yake, tayi kwalliya abinta tayi kyau, yaranta na dawowa makaranta suka ci abinci tayi masu wanka.

Tun daga bakin gate aliyu ya soma ganin canji ganin harabar gidan a share ba wata qaxanta, yayi parking motar sa ya nufi cikin gidan,

Yayi mamakin jin ta rungume sa tana masa oyoyo abinda ya dade bai sami hakan ba, ya qara daure fuskar sa, baiyi magana ba ya soma tafiya.

Tayi qoqarin karbar ledar dake hannunsa tana dubawa, kaxa ce guda biyu a ciki, godia ta riqa masa har dasu addua, ta dauki kayan ta saka a fridge kana ta gabatar masa da abinci.
Duk abinda take mamakinta yake, yaga sauyawa sosai a tattare da ita har yake qara godewa kuluwa domin itace ta bashi wannan shawarar kasancewar ba auren ta xaiyi ba an riga an mata miji.

Tun daga lokacin Safiya ke tattalin aliyu da nuna masa soyayya, duk abinda ya kawo bata rainasa komi qanqantarsa xata karba da hannu biyu tana masa godia.

'Ko da taji maganar auren da yake wasa yake ta qara rungumeshi cikin farin ciki tana godewa Allah.

Sirrin gidanta da mijinta ta daina gayawa kowa, ta dauki auren ta da daraja fiye da komai a duniya kuma tana kula da mijinta sosai.

SHAWARA GA WADANNAN MATAN MASU HANGEN NESA SHINE SU SAKAWA ZUCIYARSU HAKURI DA ABUNDA KE GARESU,, SANNAN SU KALLI NA K'ASANSU BA WANDA YAKE SAMANSU BA SABODA KOMAI TALAUCINKA AKWAE WANDA YA FIKA AKWAE WANDA KAFI WADATA, SU SAKAWA RANSU CEWA AKWAE WADANDA KE MURADIN ZAMA TAMKARSU, SU GUJI KYALE KYALEN DUNIYA SANNAN GUJI KAWAYEN BANZA DON ZASU KAISU SU BARASU WADANDA SUKA DAUKI RAYUWARSU DA ZAFI,SU DAINA HANGEN ABUNDA WANI SU RUMTSE IDANUNSU, SU SAWA KANSU DANGANA DA RASHI DA SAMU SANNAN SU KASANCE MASU GODIYA DA ABUNDA SUKA SAMU INDAE SUNA SON ZAMAN LAFIYA A TARE DASU, A RIQA HAQURI DA ABINDA MIJI YA KAWO BAA SAN YANDA YA WAHALA YA XO DA ABIN BA, A RIQA GODIYA DA NUNA FARIN CIKI AKAN DUK ABINDA YAXO DASHI GIDA, A DAINA GANIN 'NA WANCE 'KO ANAYI WA WANCE ABU NI BAA MIN, ALLAH YASA MUGANE HAKA, MASU YI KUMA ALLAH YA SHIYESU.

Follow me on Wattpad, Pherty-xarah ... ❤

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now